Bahallatsar naira biliyan 6.3: Kotu za ta yanke hukunci ga wani tsohon gwmanan Najeriya a yau

Bahallatsar naira biliyan 6.3: Kotu za ta yanke hukunci ga wani tsohon gwmanan Najeriya a yau

A yau Laraba 5 ga watan Daisamba ne babbar kotun jahar Filato za ta yanke hukunci a shari’ar da take sauraro tsakanin tsohon gwamnan jahar Filato, Sanata Jonah Jang da hukumar yaki da rashawa ta yi ma tattalin arzikin kasazagon kasa, EFCC.

Idan za’a tuna EFCC ta maka Janga gaban kotu ne akan tuhmarsa da take yi da wawure naira biliyan shida da miliyan dari uku, N6,300,000,000, tare da hadin gwiwar akawun kudi a ofishin sakataren gwamnatin jahar, Pam Yusuf.

KU KARANTA: Boko haram: Buhari ya umarci shugaban hafsoshin sojan sama da ya tare a Borno

Alkalin kotun mai sharia Daniel Longji ne ya sanar da dage karar a kwanakin baya biyo bayan cece kuce daya barke tsakanin lauyoyin EFCC a karkashin jagorancin Rotimi Jacobs da lauyoyin wadanda ake kara a karkashin jagorancin Mike Ozekhome.

Da fari dai lauya mai kara ne ya fara bayyana ma kotu guda daga shaidunsa guda uku don ya bada bayani game da abinda ya sani game da wata wasika da bankin Zenith ta aika ma EFCC, a ranar Talata inda a cikin wasikar ta tabbatar da Jang ne ya amshi kudin ta hannun Pam.

Sai dai lauyan Jang, Mike ya nuna rashin amincewarsa da bayanan shaidan, inda ya dangantan matsayinsa da cewa mutumin da EFCC ta dauko daga bankin Zenith a matsayin shaida, Emmanuel Kanja, ba shien ya rubuta wasikar da bankin ta aika ma EFCC ba.

Haka zalika a cewar lauya Mike, shaidan baya cikin wadanda suka sanya hannu akan wasikar, don haka bai cancanci ya bada shaida akan wanda ake kara ba, sai dai a samo wani daga cikin wadanda suka rubuta wasikar ko kuma ya sanya hannu akanta.

Daga karshe Alkali mai sharia Daniel Longji y adage sauraron karar zuwa ranar Laraba 5 ga watan Nuwamba don yanke hukunci akan jayayyar dake ta shiga tsakanin lauyoyin bangarorin biyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel