BMO ta nemi APC ta haramtawa gwamnonin jam'iyyar 2 yin takarar sanata

BMO ta nemi APC ta haramtawa gwamnonin jam'iyyar 2 yin takarar sanata

Kungiyar masu tallata takarar shugaban kasa, Muhammadu Buhari (BMO) sun nemi jam'iyyar APC ta kwace tikitin takarar Sanata daga hannun gwamnonin jihohin Imo da Ogun.

BMO ta bayar da wannan shawara ne bayan gwamnonin sun bayyana goyon bayansu ga 'yan takarar su na gwamna da su ka canja sheka zuwa wasu jam'iyyun bayan basu samu tikitin takarar gwamna a jam'iyyar APC ba.

Kamar yadda Legit.ng ta sanar da ku a daya daga cikin labaranta, kun ji cewar Uche Nwosu, tsohon shugaban ma'aikatan jihar Imo kuma suruki ga gwamna Rochas dake neman takarar gwamna a APC ya canja sheka zuwa jam'iyyar AA.

Hakan ta fito fili a bayyane ne bayan wayar gari da ganin fastocin Nwosu tare da na shugaba sun mamaye ko ina a jihar Imo tun ranar Lahadin makon jiya.

BMO ta nemi APC ta haramtawa gwamnonin jam'iyyar 2 yin takarar sanata

Gwamnonin APC
Source: Depositphotos

Faruwar hakan ta kawo karshen duk wani hasashe da canki-in-canka a kan makomar surikin na Rochas bayan jam'iyyar APC ta hana shi tikitin takarar gwamna.

Rochas Okorocha ne ya kafa jam'iyyar AA kafin ya canja sheka zuwa PDP, sannan daga bisani ya koma APC.

A nasa bangaren, gwamnan jihar Ogun,m Sanata Ibikunle Amosun, ya bayyana cewar dan takarar sa da APC ta hana tikitin takarar gwamna, Adekunle Akinlade, ya yi daidai da canja sheka zuwa jam'iyyar APM.

Duk da daurin gindin gwamna da yake da shi, Akinlade ya sha kasa a hannun attajirin dan kasuwar man fetur, Dapo Abiodun, a zaben fidda 'yan takara na jam'iyyar APC.

DUBA WANNAN: Gangamin Atiku: 'Kan mage ya waye' - Sakon matasan Sokoto ga PDP

Akinlade ya ce ya canja sheka zuwa jam'iyyar APM tare da 'yan majalisar dokokin jihar Ogun 26 a yau, Litinin.

Fusatattun mambobin jam'iyyar ta APC a jihar Ogun sun bayyana, ta bakin kakakinsu, Lamidi Olatunji, cewar sun canja sheka zuwa jam'iyyar APM ne domin cika burinsu na yin takara bayan an yi ma su fashin tikitin takara a APC.

Ma su canja shekar da dan takarar gwamnan da su ka hada Dayo Adeneye (kwamishinan yada labarai) da Modupe Mujota (kwamishinan ilimi), sun shiga ganawa da Amosun jim kadan bayan sanar da ficewar su daga APC.

Da yake magana yayin ganawar ta su, Amosun ya bayyana cewar sau 28 yana ganawa da Buhari da shugabannin jam'iyyar APC a kan rikicin tikitin takarar gwamna a jihar Ogun.

A ranar 31 ga watan Janairu ne hukumar zabe za ta fitar da jerin sunayen 'yan takara a kowacce jam'iyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel