Shehu Sani ya maidawa El-Rufai martani game da gangamin PDP

Shehu Sani ya maidawa El-Rufai martani game da gangamin PDP

- Kwanan nan Jam’iyyar hamayya ta PDP tayi wani babban gangami a Garin Sokoto

- Gwamna Kaduna Nasir El-Rufai ya ce akwai Sojojin gona daga Nijar cikin zugar PDP

- Sanata Shehu Sani ya maida martani inda yace APC ta aro jama’a daga Kasar Sudan

Shehu Sani ya maidawa El-Rufai martani game da gangamin PDP

Shehu Sani ya fadawa APC su aro mutane daga Sudan idan sun tashi kamfe
Source: UGC

Mun samu labari cewa Gwamna Nasir El-Rufai ya tsoma baki game da babban gangamin da Jam’iyyar PDP ta shirya na Yankin Arewa maso Yamma a Garin Sokoto. Gwamnan yace PDP tayi hayar Sojojin gona a wajen taron.

Sanatan Kaduna na tsakiya watau Shehu Sani wanda Abokin hamayyar Gwamnan ne ya maida martani a kaikaice game da wannan batu. Sanata Shehu Sani ya maida martanin ne ta shafin sa na sadarwa na Tuwita ba da dadewa ba.

Shehu Sani wanda ya bar Jam’iyyar APC kwanaki ya koma PRP ya bayyana cewa idan har Jam’iyyar PDP tayi aron jama’a daga Jamhuriyar Nijar kamar yadda ake rayawa, ya kamata ace APC kuma ta nemo mutane daga Sudan.

KU KARANTA: Jibril Al-Sudani: Atiku ya watsawa masu cewa an dauki siffar Buhari kasa a ido

Sanatan yace babu mamaki kusancin Kasar Nijar da Garin Sokoto ya sa Jam’iyyar hamayyar ta dauko mutane daga can. ‘Dan Majalisar Dattawan yayi kira ga APC ta daina kokawa game da hakan ta dauko aron jama’a daga Sudan.

Sani yake cewa akwai alaka tsakanin Jam’iyyar APC da kuma Kasar ta Sudan. Babu mamaki dai Sanatan yana nufin rade-radin da ake yi na cewa an kirkiri mutum-mutumin Shugaban kasa Muhammadu Buhari daga Kasar Sudan.

Idan ba ku manta ba, kwana nan Sanatan na PRP ya bayyana cewa ya je Sudan inda ya gana da manyan Kasar wadanda su ka tabbatar masa da cewa babu wani Jibril Al-Sudan da aka dauko mai kama da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel