Kungiyar CAN za ta shirya muhawara tsakanin Buhari da Atiku a ranar 10 ga wata

Kungiyar CAN za ta shirya muhawara tsakanin Buhari da Atiku a ranar 10 ga wata

A kokarinta na inganta yakin neman zaben shekarar 2019 don ta karkata wajen tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin yan Najeriya ba wai cece kuce, zagin juna da cin zarafin juna ba, kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, za ta shirya muhawara tsakanin yan takarar shugaban kasar Najeriya.

Majiyar Legit.com ta ruwaito hukumar CAN za ta shirya muhawarar ne tare da hadin gwiwar wata kungiya mai zaman kanta, Legacy Initiative International, kamar yadda shugaban kungiyar, Kenny Martins ya bayyana.

KU KARANTA: Gwamnatin jahar Zamfara ta raba ma Sojojin sa-kai Babura 850 don yaki da yan bindiga

Mista Kenny Martins ya bayyana haka ne a ranar Talata 4 ga watan Disamba yayin da yake ganawa da manema labaru a jahar Legas, wanda yace sun shirya mahawarar ne da hadin gwiwar CAN don tabbatar da an tattauna abubuwan da suka shafi yan Najeriya.

A cewar Martins, sun shirya mika al’amuran zaben shekarar 2019 ga ubangiji Allah ne, don haka zasu fara da gudanar da taron addu’o’I daga ranar 10 ga watan Janairu a karkashin jagorancin shugaban CAN, Supo Ayokunle.

“Haka zalika shirye shirye sun yi nisa tsakanin da yan uwanmu Musulmai don gabatar da addu’o’i a babban birnin tarayya Abuja da kuma jahar Legas, manufar hakanshine don wayar da kawunan dukkanin yan Najeriya ga cewa duk abinda ya faru a zaben 2019 yin Allah ne.” Inji shi.

Daga karshe Martinsa yace suna addu’ar Allah ya dawwamar da zaman lafiya da cigaba mai daurewa a Najeriya daga yanzu har zuwa zaben shekarar 2019, da ma har bayan zaben 2019.

A wani labarin kuma n tashi baram baram ba tare da cimma matsaya ba a zaman tattaunawa daya gudana tsakanin kungiyar Malaman jami’o’in Najeriya, ASUU, da gwamnatin Najeriya akan yajin aiki na dindindin da ASUU ta shiga tun kimanin wata daya da ya shude.

An gudanar da wannan zama ne a ranar Talata 4 ga watan Disamba a ofishin ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, wanda ya gayyaci yayan kungiyar ASUU don tattauna hanyoyin shawon kan matsalolin da suke fama dasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel