2019: Obasanjo, Atiku, Secondus sun sake ganawa a garin Abuja

2019: Obasanjo, Atiku, Secondus sun sake ganawa a garin Abuja

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu cewa a daren jiya na Laraba cikin garin Abuja, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya yi wata ganawar sirrance da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Jaridar The Punch ta kuma ruwaito, wannan ganawa da ta gudana cikin garin Abuja ta hadar da shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Prince Uche Secondus, da kuma wasu amintattun mambobin na jam'iyyar.

Majiyar rahoton da ta zayyanawa manema labarai ta bayyana cewa, ganawar ta gudana domin shimfida dabaru gami da tsare-tsare na tabbatar da nasarar Atiku da jam'iyyarsa ta PDP yayin babban zabe na 2019.

2019: Obasanjo, Atiku, Secondus sun sake ganawa a garin Abuja

2019: Obasanjo, Atiku, Secondus sun sake ganawa a garin Abuja
Source: Depositphotos

Kazalika ganawar ta gudana domin sake nazari da kulla tsare-tsare dangane da salon dabaru mafiya kyawu da inganci wajen gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar cikin shiyoyin kasar nan.

Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon shugaban kasa Obasanjo ya ribaci wannan ganawa domin sulhunta dambarwa ta takun sakar siyasa da ke tsakanin Atiku da kuma tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako.

KARANTA KUMA: 2019: An nemi jam'iyyar PDP ta sauya dan takarar shugaban kasa

Baya ga Nyako, tsohon shugaban kasar ya nuna hali na dattako wajen sulhunta rashin fahimtar juna da ke tsakanin Atiku da kuma tsohon hadiminsa yayin da ya ke rike da kujerar mataimakin shugaban kasa, Dakta Umar Ardo.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a ranar Litinin din da ta gabata dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya kaddamar da yakin sa na neman zabe a jihar Sakkwato da ko shakka ba bu ido ba mudu ya tabbatar da karbuwarsa a shiyyar Arewa maso Yamma.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel