Buhari ya bayyana bacin ransa da barkewar rikici a jihar Kuros Riba

Buhari ya bayyana bacin ransa da barkewar rikici a jihar Kuros Riba

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nuna damuwa da rashin jin dadinsa dangane da wani rikici mai nasaba da kabilanci da ya barke a jihar Kuros Riba.

A yau, Talata, ne rahotanni a Najeriya su ka bayyana cewar wani rikici ya barke a tsakanin wasu al'ummomi 4 da ke karamar hukumar Biase a jihar Kuros Riba.

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana, rikicin ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane da kuma kone gidaje fiye da 100, lamarin da ya kai ga wasu mazauna yankin na guduwa zuwa wasu garuruwa da ke makwabtaka da su.

Shugaba ya yi kira ga masu rikicin da su zauna lafiya da juna a yankinsu mai makwabtaka da jihar Abiya.

Buhari ya bayyana bacin ransa da barkewar rikici a jihar Kuros Riba

Buhari
Source: Twitter

"Ya kamata wadannan al'ummomi su rungumi sulhu domin samun zaman lafiya, ba za a taba samun cigaba a wurin da babu zaman lafiya ba," a kalaman shugaba Buhari.

DUBA WANNAN: Ana shiryawa Buhari tuggu - Osinbajo

Kazalika ya jinjinawa kokarin gwamnatin jihar ta Kuros Riba bisa daukan matakin gaggawa a kan rikicin. Ya kuma jinjinawa rundunar 'yan sanda ta jihar bisa yadda suka gaggauta turo jami'ansu zuwa yankin da rikicin ya barke.

Ko a watannin baya da suka wuce an samu barkewar wani rikici kwatankwacin irin wannan a tsakanin wata kabila da ke jihar Kuros Riba da makwabciyar ta dake jihar Ebonyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel