Gwamnatin jahar Zamfara ta raba ma Sojojin sa-kai Babura 850 don yaki da yan bindiga

Gwamnatin jahar Zamfara ta raba ma Sojojin sa-kai Babura 850 don yaki da yan bindiga

Gwamnatin jahar Zamfara a karkashin jagorancin Gwamna Abdul Aziz Yari ta sayo sabbin babura guda dsari takwas da hamsin, 850, tare da mikasu ga kungiyar Sojojin sa-kai da aka fi sani da suna Civilian JTF don taimakawa wajen yaki da ayyukan yan bindiga.

Legit.com ta ruwaito kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Alhaji Bello Dankande ne ya bayyana haka a yayin da yake rarraba baburan a ranar Talata 4 ga watan Nuwamba, inda yace gwamnati ta ga dacewar raba baburan ga kungiyar ne saboda muhimmin rawar da suke takawa wajen yaki da yan bindiga a jahar.

KU KARANTA: Yansanda sun kama wata Mata da ta jefar da jaririnta a Gombe

Kwamishinan yace an raba babura hamsin hamsin ga kowacce masarauta, kuma an daura hakkin kula da sanya idanu akan baburan ga kowanne Sarkin yankin, haka zalika gwamnatin ta bayar da naira dubu dari biyar biyar ga duk masarauta don kulawa da baburan.

Bugu da kari, kwamishina Dankande ya bada tabbacin manufar gwamnatin jahar Zamfara na cigaba da yaki da satar shanu da matsalar garkuwa da mutane a jahar har sai zaman lafiya da kwanciyar hankali ya samu a jahar.

A jawabinsa, Sarkin Anka, Attahiru Ahmed yay aba ma gwamnatocin kananan hukumomin jahar Zamfara da gwamnatin jahar kanta da ma gwamnatin tarayya bisa kokarin da suke yin a magance matsalar tsaro a jahar.

Sarkin ya yaba da karin adadin dakarun Sojoji da na sauran jami’an tsaro da gwamnatin tarayya ta jibge a jahar don yaki da yan bindiga, barayin shanu da masu garkuwa da mutane, amma yayi kira a gareta data tura jami’an zuwa yankunan da suka fi shi zama cikin hadari.

“Duk da adadin jami’an tsaron dake jahar, har yanzu ana cigaba da samun matsalar satar mutane, don haka nake kira ga gwamnatoci a dukkanin matakai dasu zage damtse wajen shawokan matsalar da ake fama da ita.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel