2019: An nemi jam'iyyar PDP ta sauya dan takarar shugaban kasa

2019: An nemi jam'iyyar PDP ta sauya dan takarar shugaban kasa

Daya daga cikin manema tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Mista Stanley Osifo, ya yi barazanar tayar da zaune muddin jam'iyyarsa ta gaza wajen sauya dan takararta na kujerar shugaban kasa a yayin babban zabe na 2019, Atiku Abubakar.

Mun samu cewa, Mista Stanley ya bayar da wa'adin kwanaki 2 ga jam'iyyar kan gaggauta watsar da Atiku a matsayin dan takarar ta tare da yin kira kan aiwatar da wani sabon zaben fidda gwanin takara na jam'iyyar.

Osifo ya kuma yi barazanar gurfanar da jam'iyyar sa gaban Kuliya muddin ta gaza wajen tabbatar da wannan bukata da ya gindaya ta watsar da Atiku a matsayin gwanin ta na takara da kuma kiransa sake gudanar da sabon zaben fidda gwani.

Atiku yayi kaddamar da yakinsa na neman zabe cikin Birnin Shehu a jiya Litinin

Atiku yayi kaddamar da yakinsa na neman zabe cikin Birnin Shehu a jiya Litinin
Source: Facebook

Yayin ganawarsa da manema labarai cikin birnin Legas, Osifo ya bayyana cewa, dukkanin manema tikitin takara na jam'iyyar na cikakken alhaki na samun dama tamkar ta Atiku da a cewar sa kowanen su ya mallaki takardun neman kudirin takara daidai da na Atiku.

Dan takarar da ya kasance haifaffen jihar Edo ya bayyana cewa, takaicin sa ya takaita ne kadai dangane da ya yadda ya zubawa Sarautar Mai Duka idanu wajen halarta tare da shiga cikin sahun tantance manema tikitin takara da jam'iyyar ta gudanar yayin zaben ta na fidda na gwani.

KARANTA KUMA: Hadimar Shugaban 'Kasa Buhari ta yada wani rahoto na 'Karya kan Atiku

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, jam'iyyar ta PDP ta gudanar da zaben ta na fidda gwanayen takarar cikin farfajiyar wasanni ta Adokiye Amiesimaka da ke birnin Fatakwal na jihar Rivers a raar 6 ga watan Oktoba da ya gabace mu.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito, a jiya Litinin, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku, ya kaddamar da yakin sa na neman zabe kan takarar kujerar shugaban kasa karkashin inuwa ta jam'iyyar PDP can jihar Sakkwato.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel