Yansanda sun kama wata Mata da ta jefar da jaririnta a Gombe

Yansanda sun kama wata Mata da ta jefar da jaririnta a Gombe

Rundunar Yansandan jahar Gombe ta yi ram da wata mata mai shekaru 24, Mariya Yakubu da laifin jefar da danta sabon jariri a cikin wasu rukunin gidaje dake cikin garin Gombe, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito kwamishinan Yansandan jahar Gombe, Muhammad Garba Mukaddas ta bayyana cewa Mariya ta jefar da jaririn ne a ranar 24 ga watan Nuwamba a rukunin gidajen Manawashi.

KU KARANTA: Kalli yadda ma’aikata suka wulakanta shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki

Kwamishina Mukaddas yace wani mutumi dake bin hanyar ne ya baiwa Yansanda rahoton tsintar jaririn, inda yace samun rahoton tsintar jaririn keda wuya sai ya umarci Yansandan Low-cost su garzaya inda aka jefar jaririn.

Amma har sai a ranar 29 ga watan Nuwamba ne yansanda suka bi diddigin matar, inda suka samu nasarar kamata ta hanyar samun bayanan sirri, haka zalika yace jaririn na cikin koshin lafiya da samun kyakkyawar kulawa a hannun Yansanda.

Sai dai kwamishina Mukaddas yace Mariya ta amsa laifinta, daga nan kuma ya nemi jama’an gari su cigaba da taimaka musu da bayanan sirri da zasu taimaka musu wajen kama miyagun mutane tare da magance miyagun laifuka.

“Ina tabbatar ma jama’a ba zamu boye sunayen duk wadanda suka bamu sahihan bayanai, haka zalika zamu yi amfani da bayanan ta hanyar da kamata, wannan alkawari ne muka dauka.” Inji shi.

A wani labarin kuma rundunar Yansandan jahar Osun ta yi ram da wani Limamin Masallaci da abokansa guda uku da laifin satar wani mutum, Victor Akinbile tare da kasheshi ba tare da wani hakki ba, sai dai kawai don ya kasa biyansu naira miliyan uku kudin fansa.

Kwamishinan Yansandan jahar, Fimihan Adeoye ne ya sanar da haka ne a ranar Talata 4 ga watan Nuwamba inda ya bayyana sunayen mutanen kamar Liman Bashir Owolabi, Rafiu Ahmed, Sunday Kayode da Rasheed Waheed.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa-

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel