Yanzu-yanzu: Kotu ta umurci EFCC, DSS da 'Yan sanda su kamo Diezani cikin sa'a 72

Yanzu-yanzu: Kotu ta umurci EFCC, DSS da 'Yan sanda su kamo Diezani cikin sa'a 72

Wata babban kotun tarayya ta bayar da umurni da hukumomin EFCC, DSS da 'yan sandan Najeriya sun gabatar da tsohon ministan man fetur, Diezani Allison Madueke cikin kwanaki uku kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Tsohuwar ministan da ke zaune a Landan ta dade hukumar yaki masu yiwa arzikin kasa ta'annati EFCC tana bincikar ta kuma cikin kwanan nan ta fara duba yiwuwar dawo da ita Najeriya domin ta fuskanci shari'a.

Mai shari'a Valentine Ashi na babban kotun tarayya da ke zamanta a Apo, Abuja ne ya bawa hukumomin tsaron Najeriya umurnin su gabatar da Diezani a gaban kotun cikin sa'a 72 a yau 4 ga watan Disamba.

Yanzu-yanzu: Kotu ta umurci EFCC, DSS da 'Yan sanda su gabatar da Diezani a gabatan cikin sa'a 72

Yanzu-yanzu: Kotu ta umurci EFCC, DSS da 'Yan sanda su gabatar da Diezani a gabatan cikin sa'a 72
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: A bamu makamai mu yaki 'yan ta'adda - Babban Sarki a Zamfara ya roki Buhari

Ya bayar da umurnin ne bayan lauyan EFCC, Msuur Denga ya shigar da bukatarsa ga kotun na rokonta ta bayar da izinin kama Diezani domin hukumar ta samu damar gurfanar da ita gaban kuliya bisa zargin karkatar da kudade a Najeriya.

EFCC na binciki tsohuwar ministan ne tare da Jide Omokore, tsohon ciyaman din Atlantic Energy Drilling Company, bayan Coalition Against Corrupt Leaders, CACOL ta shigar da kara a kansu a ranar 2 ga watan Oktoban 2013 na zarginsu da rashawa da satar kudade.

Binciken da aka gudanar sun nuna cewa tsohuwar ministan da ke kulawa da hukumar NNPC ta aikata wasu cinikayya ba bisa ka'ida ba a madadin gwamnatin tarayya na wancan lokacin.

Lauyan EFCC ya shaidawa kotu cewa Diezani ta fice daga Najeriya ne a lokacin da ake gudanar da bincike a kanta.

"A madadin shugaban kasar Najeriya, ina umurtar sufeta janar na 'yan sanda, Ciyaman din EFCC, Attorney Janar da hukumar DSS suka kamo wadda ake tuhumar su gabatar da ita gaban kotu a cikin sa'o'i 72," inji Alkali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel