Zaben 2019: Ku kasance cikin shirin ko ta kwana da jiran tsammani - Hukumar 'Yan sanda ga jami'anta

Zaben 2019: Ku kasance cikin shirin ko ta kwana da jiran tsammani - Hukumar 'Yan sanda ga jami'anta

A yayin da yakin neman zabe ya kanannade duk wani kwararo da lungunan kasar nan ta Najeriya, hukumar 'yan sanda ta gindaya gargadi ga jami'anta kan kasancewarsu cikin shirin sauke nauyin bayar da tsaro da ya rataya a wuyansu.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, hukumar ta kuma gargadi jami'an na ta tare da neman su kan kasancewa da kuma zama cikin shiri na jiran tsammani da ko ta kwana tamkar a filin Yaki domin kare martaba da baiwa kasar nan kariya gami da tsaro.

Mataimakin Sufeto Janar na 'Yan sanda shiyya ta 8, Adekunle Oladunjoye, shine ya bayyana hakan a yau Talata yayin shawagin da ya gudanar cikin birnin Ilorin domin samun sanayya kan rassa da cibiyoyin hukumar 'yan sanda na jihar Kwara.

Zaben 2019: Ku kasance cikin shirin ko ta kwana da jiran tsammani - Hukumar 'Yan sanda ga jami'anta

Zaben 2019: Ku kasance cikin shirin ko ta kwana da jiran tsammani - Hukumar 'Yan sanda ga jami'anta
Source: UGC

Majiyar jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, shiyya ta takwas ta hukumar 'yan sanda ta kunshi rassa da kuma cibiyoyin ta da ke jihar Kogi, Kwara da jihar Ekiti.

AIG din na 'yan sanda ya kuma gargadi jami'an sa kan tabbatar da yiwa dokokin kasar nan da'a tare da neman hadin kan al'ummar kasar nan da a cewarsa hakan ya zamto wani cikamako na amincin sauke nauyin da rataya a wuyansu.

KARANTA KUMA: Sake zaben Buhari lamari ne da ya zamto tilas - Tinubu

AIG Oladunjoye ya kuma gargadi jami'an na 'yan sanda kan ribatuwa da makamansu da kuma kayan aiki ta hanya mafi kyawun gaske da kuma kwazo wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na kare martabar kasa.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, rayukan Mutane biyar sun salwanta yayin da gidaje da dama suka kone kurmus sakamakon wani rikicin kabilanci da ya barke a jihar Cross River.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel