Kalli yadda ma’aikata suka wulakanta shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki

Kalli yadda ma’aikata suka wulakanta shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki

Rai ya baci, kuma hankula sun tashi yayin da ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya suka yi bore a ranar Talata 4 ga watan Disamba a harabar majalisar, wanda ta kai ga sun hana yan majalisa shiga ofisoshinsu, sa’annan suka yi ma shugaban majalisar, Sanata Bukola Saraki ihu.

Jaridar The Cable ta ruwaito Sanata Saraki ya gamu da fushin ma’aikatan majalisar ne a yayin da yake gabatar da jawabi a garesu, inda ya nemi su kwantar da hankulansu game da zanga zangar da suke yi akan rashin samun albashinsu.

KU KARANTA: Wani Limamin Masallaci ya yi garkuwa da bawan Allah, har sai da ya kasheshi

Sai dai a yayin da yake jawabin nasa, sai ma’aikatan suka shiga yi masa eho suna cewa “Idan ba’a biyamu albashinmu ba, toh babu sauran zaman majalisa” haka suka cigaba da ihu har zuwa karshen jawabinsa.

A jawabin nasa, Saraki ya baiwa ma’aikatan hakuri, inda yace su bashi daga yau zuwa ranar Juma’a mai zuwa zai shawo kan matsalar, domin a cewarsa amfanin majalisa ne ace ma’aikatanta suna cikin halin kyakkyawar walwala.

Da safiyar Talata 4 ga watan Disamba ne ma’aikatan suka yi ma majalisar tsinke suna gudanar zanga zanga akan rashin samun hakkokinsu da suka hada da karin albashi, da sauran alawus alawus da suke bin hukumar majalisar bashi tun shekarar 2010.

Wadannan korafe korafe ne yasa ma’aikatan suka nemi akawun majalisar Sani Omolari ya yi murabus daga mukaminsa saboda ya gaza kare hakkokinsu, da kuma zarginsa da suke yin a rike hakkokinsu.

Sai dai a nasa jawabin, Omolori ya bayyana ma ma’aikatan cewa ba daidai bane su hana yan majalisar zama don su gudanar da aikinsu kawai don suna zanga zanga, haka zalika ya musanta batun cewa wai ya rike musu kudadensu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel