Jigon PDP a Adamawa, Tahir ya sauya sheka zuwa APC

Jigon PDP a Adamawa, Tahir ya sauya sheka zuwa APC

Alhaji Sa’ad Tahir, wani jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party( PDP) a jihar Adamawa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressive Congress (APC) .

Gwamna Mohammed Bindow na Adamawa ya tabbatar da lamarin a lokacin nadin Menene Buhari-Bindow Ne 2019, ofishin kamfen din arewa maso gabas a ranar Talata, 4 ga watan Disamba.

Bindow ya bayyana sauya shekar tsohon dan takarar gwamnan na PDP tare da wasu masu ruwa da tsaki na PDP a jihar a matsayin nasara ga APC a zaben 2019.

Jigon PDP a Adamawa, Tahir ya sauya sheka zuwa APC

Jigon PDP a Adamawa, Tahir ya sauya sheka zuwa APC
Source: Depositphotos

Ya ce APC a jihar za ta sanya rana domin yin kwarya-kwaryan walima na masu sauya shekar.

KU KARANTA KUMA: Hayan mutane PDP suka yi daga kasar Nijar a gangamin jam’iyyar su - El-Rufai

A nashi jawabin, Tahir wanda ya kasance mataimakin tsohon gwamna, Bala Ngillari, ya bayyana cewa yanzu hankalin shi ya kwanta a sabuwar jam’iyyarsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel