Har yanzu babu dan takarar shugaban kasa sahihi - Babban malamin addini

Har yanzu babu dan takarar shugaban kasa sahihi - Babban malamin addini

Archbishop din mabiyar darikar Katolika na Abuja, Cardinal Onaiyekan ya ce 'yan Najeriya sun tsinci kansu cikin tsaka mai wuya a kan batun dan takarar shugabancin kasa da za su zaba a shekarar 2019.

Malamin addinin Kiristan ya yi magana ne karshen makon da ya wuce a Abuja a wani taro da Catholic Action ta shirya.

A cewarsa, ya ce ba dai-dai bane cocin da rabe bayan jam'iyya guda sai dai abinda ya kamata shine ta binciko 'yan takarar da suke da tsare-tsare masu kyau ta goyi bayansu.

Ya ce sabbin jam'iyyun siyasa suna da damar hadin gwiwa wajen fitar da ingantaccen dan takarar shugabancin kasa baya ga na jam'iyyun APC da PDP amma girman kai da kwadiya ba zai bari su aikata hakan ba.

Har yanzu babu dan takarar shugaban kasa sahihi - Babban malamin addini

Har yanzu babu dan takarar shugaban kasa sahihi - Babban malamin addini
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Yadda Saraki ya ci amanar mu a kan biyan bukatar sa - Tinubu

"Abin ya fito fili karara a Najeriya. Mukan ji 'yan siyasa na cewa suna neman mulki ne don yiwa kasa hidima. Kowa ya gane wannan karya ce. Har mutanen karkara ma sun gane wadanda ke rike da madafin iko ba mu suke yiwa aiki ba. Wannan shine babban matsalar mu. Shugabani suna zama masu kama karya a maimakon masu yiwa al'umma hidima.

"Kallon da mafi yawancin al'umma suke yiwa siyasa a matsayin sana'ar makaryata kuskure ne duk da mun san cewa yana da wahala samun masu riko da gaskiyar. Tsoron da al'umma keyi shine wasu tsirarun marasa son gaskiya da suka samu mulki ta hanyar magudi sun rike arzikin kasar. Su suke juya akalar kasar," a cewarsa.

Onaiyekan ya ce Najeriya ta tsinci kanta cikin babban matsalar a yanzu da ake fuskantar zaben 2019 saboda bisa alamu zabin da ya rage wa 'yan Najeriya shine 'yan takara biyu da duk an gaji da su.

"Abin tausayi ne duba da yadda muke da jam'iyyun siyasa sama da 90 amma babu wani zabi bayan manyan jam'iyyun guda biyu da duk sun gaza cika mana alkawurran da suka dauka. Bayansu wane zamu zaba? Abin takaici ne yadda sauran jam'iyyun suka gaza hada kai waje guda domin fitar da dan takarar shugabancin kasa," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel