Ma su zanga-zanga sun hana sanatoci da 'yan majalisar wakilai zaman majalisa

Ma su zanga-zanga sun hana sanatoci da 'yan majalisar wakilai zaman majalisa

Zanga-zangar fusatattun ma'aikatan majalisar tarayyar Najeriya sun hana sanatoci da mambobin majalisar wakilai zaman majalisa na yau.

Ma su zanga-zanga sun yi kunnen uwar shegu da kalaman mambobin majalisar da su ka yi yunkurin ba su baki domin su bar bakin kofar shiga zauren majalisar.

Fusatattun ma su zanga-zangar kan kaure da ihu ga duk mamba a majalisar wakilai ko ta dattijai da ya yi kokarin ya lallaba su.

Ma su zanga-zanga sun hana sanatoci da 'yan majalisar wakilai zaman majalisa

Ma su zanga-zanga sun hana sanatoci da 'yan majalisar wakilai zaman majalisa
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: A bamu makamai mu yaki 'yan ta'adda - Babban Sarki a Zamfara ya roki Buhari

Sun hana mambobin majalisar dattijai zamansu na yau da ya kamata su yi da misalin 10:00 na safe, kazalika sun hana mambobin majalisar wakilai na su zaman da zasu yi da karfe 11:00 na safe.

Amma har misalin karfe 12:40 na rana, babu mamba da ya iya samun damar shiga cikin ginin majalisar balle har ta kai ga 'yan majalisar sun shiga zauren majalisar domin yin zamansu na yau.

Ma su zanga-zangar sun yi ikirarin cewar ba zasu bari majalisar ta yi wani zama ba a cikin wannan satin, matukar ba a biya su dukkan albashi da alawus da su ke bin majalisar bashi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel