Sake zaben Buhari lamari ne da ya zamto tilas - Tinubu

Sake zaben Buhari lamari ne da ya zamto tilas - Tinubu

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya zayyana cewa sake zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin babban zabe na 2019 lamari ne da ya riga da kasancewa wajibi kuma tilas.

Ya nemi daukacin al'ummar kasar kan kauracewa zaben jam'iyyar adawa ta PDP da kuma dan takararta na kujerar shugaban kasa, Atiku Abubakar, kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito.

Tinubu ya nemi al'ummar kasar nan kan haramtawa jam'iyyar PDP dawowa kan karagar mulkin kasar nan sakamakon yadda ta shafe shekaru 16 ba tare da fidda kasar nan zuwa ga tudun tsira illa iyaka da ta jefa ta cikin kangi na gurbatanci.

Sake zaben Buhari lamari ne da ya zamto tilas - Tinubu

Sake zaben Buhari lamari ne da ya zamto tilas - Tinubu
Source: Depositphotos

Tsohon gwamnan yayi fedewa jam'iyyar PDP Biri har wutsiya, ya bayyana cewa ko kusa ba ta da wata nasaba ta cancantar jagorancin kasar nan.

Majiyar jaridar ta Legit.ng ta ruwaito cewa, Tinubu ya bayyana takaicinsa kwarai da aniyya dangane da ababen tabarbarewa da jam'iyyar PDP ta yiwa kasar nan sanadi da suka hadar da rashin inganci na harkokin ilimi da kuma kiwon lafiya tare da zagwanyewar tattalin arzikin kasa.

KARANTA KUMA: Ba bu wata wahala da za a fuskanta, akwai wadataccen Man Fetur a Najeriya - NNPC

Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon gwamnan ya zayyana hakan ne cikin jawabansa ga ga babbar cibiya ta magoya bayan shugaban kasa Buhari yayin ganawarsu cikin babban birnin kasar nan na tarayya a yau Talata.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wata sanata ma wakiltar shiyyar Legas ta Tsakiya a majalisar Dattawa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa a halin yanzu an yi walkiya shugaban kasa Buhari ya bambance tsakanin Masoyansa da kuma Makiya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel