Hayan mutane PDP suka yi daga kasar Nijar a gangamin jam’iyyar su - El-Rufai

Hayan mutane PDP suka yi daga kasar Nijar a gangamin jam’iyyar su - El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya yi zargin cewa tarin mutanen da suka halarci taron gangami na jam’iyyar PDP da akayi na kaddamar da dan takarar shugaban kasan jam’iyyar, Atiku Abubabakr ba ‘yan Najeriya bane.

A cewar El-Rufai mafi yawa daga cikin su daga kasar Nijar aka yo hayan su domin cika idanu a wajen taron.

Gwamna El-Rufai ya bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da kwamitin Kamfen din jam’iyyar APC da akayi a garin Kaduna.

Hayan mutane PDP suka yi daga kasar Nijar a gangamin jam’iyyar su - El-Rufai

Hayan mutane PDP suka yi daga kasar Nijar a gangamin jam’iyyar su - El-Rufai
Source: Twitter

“Da jam’iyyar PDP ta ga cewa mutanen Sokoto ba za su halarci wannan taro ba sai suka buge da yin hayan sojojin haure, wato mutane daga Nijar.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin APC 4 na shirin barin jam’iyyar zuwa AA - Kungiya

"Za mu bi kuri’u dalla-dalla keke-da-keke domin ganin APC ta lashe zabukan 2019 a jihar Kaduna. Kuma ina so in sanar muku cewa gwamnatin Muhammadu ba gwamnatin barayi bane sannan ba gwamnati bace da za ta rika yin watandar kudi ma wasu kalilan.

Gwamnati ce da take kashe kudin ta wajen ganin ta inganta rauyukan ‘yan Najeriya," inji El-Rufai

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel