Ku taimaka ku bani gawar dana, wata guda kenan da ya rasu - wata uwa da ta rasa danta

Ku taimaka ku bani gawar dana, wata guda kenan da ya rasu - wata uwa da ta rasa danta

- Wata mata ta nemi jami'an yansanda dasu bata gawar danta

- Dan nata ya rasu ne tun watan daya gabata a yayin wani hargitsi da akayi da hukumar Customs

- Yan sandan sunce suna bincike ne suna son nemo inda bindigar su take

A Najeriya, Buhari ne zai lashe zaben 2019, inji babbar Jaridar Duniya The Economist

A Najeriya, Buhari ne zai lashe zaben 2019, inji babbar Jaridar Duniya The Economist
Source: Depositphotos

Wata mata yar shekaru 49 mai suna Mrs Esther Umukoro ta nemi jami'an yan sandan jihar Edo dasu taimaka su bata gawar danta don ta binneshi.

Mrs Umukoro tace dan nata mai suna Samson ya rasu ne a watan daya gabata a yayin wani hargitsi da aka samu da jami'an customs a kauyen Ovbiogie dake Ovia karamar hukumar jihar ta Edo.

Abun ya faru ne a watan daya gabata a bisa takunkumin bincike da NCS ta sanya biyo bayan kashe wani direban mota da akayi yayin da motar NSC ta kama da wuta.

DUBA WANNAN: Hassan Rouhani ya sake lakuce ma Trump hanci kan takunkumi

Rahoton ya bayyana cewa yaron ya rasu ne sanadiyyar wani abu daga cikin motar data kama da wuta ya bugeshi.

Matar ta kara da cewa tun daga wannan lokaci ne take zarya a hukumar yan sandan Ekiadolor don su bata gawar inda su kuma suke cewa taje ta dawo.

Yan sandan sunce har yanzu suna gudanar da bincike ne saboda wani jami'in Custom yace baiga bindigar sa.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel