Bahallastar NEMA: An fara shirin tsige Osinbajo – Dan majalisar wakilai

Bahallastar NEMA: An fara shirin tsige Osinbajo – Dan majalisar wakilai

Dan majalisar wakilan tarayya Johnson Agbonayinma (APC, Edo) ya bayyana cewa wasu yan majalisa sun fara shiryin tsige mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Game da cewarsa, yan majalisan na kokarin tsige mataimakin Buharin ne bisa ga binciken badakalar da ake zarginsa dashi na baiwa hukumar bada agaji na gaggawa wato NEMA kudi N5.8 billion wanda ya sabawa doka.

Agbonayinma wanda ya gabatar da hira da manema labarai a zauren majalisar dake Abuja cewa yanada kwakkwaran hujja cewaana shirya kaiin tsige mataimakin shugaban kasan amma bai ambaci masu wannan kaidi ba.

Yace: “ Ina mai sanar da ku cewa an fara rattaba hannu kan takarda domin tsige mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo.”

“Dalilin haka shine sakamakon binciken hukumar NEMA.”

“Ku sani cewa abubuwan da aka binciko a binciken shine badakalar kudi da dirakta janar yayi, hanyar samar da kudin, da sauransu.”

“Yayinda nike yabawa abokan aikina kan wanzar da ayyukansu kamar yadda doka ya bukata, ina rokonsu sun yi hakuri kuma su cigaba da yin abubuwan da zasu kawo zaman lafiya da hadin kai a Najeriya,”.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel