Babu wata tsiya da mulkin PDP ya tsinanawa Legas a cikin shekaru 16 - Ambode

Babu wata tsiya da mulkin PDP ya tsinanawa Legas a cikin shekaru 16 - Ambode

- Gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, ya kalubalanci mulkin da jam'iyyar PDP ta yi na tsawon shekaru 16 a kasar, wanda ta fara tun daga 199 har zuwa 2015

- Gwamnan ya ce Nigeria ba zata koma kasar Masar ba ta hanyar sake mayar da jam'iyyar PDP a mulki bayan tsallake tekun maliya da kyar

- Ya ce a cikin shekaru uku da rabi, jam'iyyar PDP ta gina tubali mai karko wanda zai farfado tare da tabbatar da dorewar tattalin arzikin kasar

Gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, ya kalubalanci mulkin da jam'iyyar PDP ta yi na tsawon shekaru 16 a kasar, wanda ta fara tun daga 199 har zuwa 2015, yana mai cewa jihar Legas bata amfana da komai ba daga wannan mulkin ba.

Ambode ya yi wannan jawabin ne a wani taron kungiyar tuntuba na kasa, karkashin kwamitin hadakar kungiyoyin da ke goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari, wacce kuma zata rinka kula da ayyukan kungiyoyin, a yunkurin ganin tazarcen shugaban kasa Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo a 2019.

Gwamnan ya ce kasar ba zata koma kasar Masar ba ta hanyar sake mayar da jam'iyyar PDP a mulki bayan da ta tsallake tekun maliya da kyar.

KARANTA WANNAN: Cin amana: Mutumin da ya damfari tsohuwar budurwasa N5m ya gurfana gaban kotu

Babu wata tsiya da mulkin PDP ya tsinanawa Legas a cikin shekaru 16 - Ambode

Babu wata tsiya da mulkin PDP ya tsinanawa Legas a cikin shekaru 16 - Ambode
Source: Depositphotos

Ya ce a cikin shekaru uku da rabi, jam'iyyar PDP ta gina tubali mai karko wanda zai farfado tare da tabbatar da dorewar tattalin arzikin kasar.

Ya ce, "Shekaru 16 da jam'iyyar PDP ta yi a mulkin kasar, karara zan iya cewa babu ta inda jihar Legas ta amfana da shi. A cikin shekaru uku da rabi kuwa, karara zan iya cewa gwamnatin APC mai ci a yau ta sa jihar Legas ta kai wani mataki na ci gaba, wanda bata samu ba shekaru 20 da suka gabata.

"Don haka, ni a nawa ganin, zai zama abu mai sauki kuma mafi a'ala idan muka rike Buhari/Osinbajo don baiwa tattalin arzikin kasar damar farfadowa da dorewa, mai makon sake barin kasar ta koma kamar Masar bayan tsallake tekun maliya, kuma tabbas na san ba zamu koma kamar kasar Masar ba."

Ya ce tunda aka rantsar da sabuwar gwamnati a 2015, gwamnatin shugaban kasa Buhari ta dauki matakai na kai kasar zuwa mataki na gaba, yana mai cewa yanzu ya ragewa 'yan Nigeria sake baiwa jam'iyyar APC damar kai kasar zuwa ga 'Mataki na gaba'.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel