Atiku ya koka bayan da babbar Jaridar Ingila tace Buhari ne zai ci zabe

Atiku ya koka bayan da babbar Jaridar Ingila tace Buhari ne zai ci zabe

- Sananniyar kamfanin jaridar The Economist ta yi hasashen cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai koma kujerar shi

- Jaridar ta yi hasashen cewa babbar jam'iyyar adawa a Najeriya zata rushe

- Amma kuma yiwuwar mutuwar ta'addancin arewa maso gabas kadan ne

Atiku ya koka bayan da babbar Jaridar Ingila tace Buhari ne zai ci zabe

Atiku ya koka bayan da babbar Jaridar Ingila tace Buhari ne zai ci zabe
Source: Twitter

Jam'iyyar adawa zata iya rushewa kafin zaben 2019 inda hakan zai bada damar komawar shugaban kasa Muhammadu Buhari kujerar shi hankali kwance.

Kamfanin jaridar ya kintato cewa yiwuwar mutuwar ta'addancin arewa maso gabas kadan ne.

Amma kamfanin yace "Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kara hayewa kujerar shi a zaben watan Fabrairu mai zuwa, saboda jam'iyyar adawa zata rushe kafin zuwan zaben."

DUBA WANNAN: Gwamnati tace a kul 'yan siyasa suka sanya zafafar lamurra kan 2019

Twitter ta cika da hasashen wanda hakan ya jawo tofin Allah tsine daga Dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar. Ya bayyana hasashen da kamfanin jaridar yayi da rashin daidaito.

A wani kalami daga mataimakin shi a harkar yada labarai, Phrank Shaibu, Atiku ya bayyana hasashen da jaridar tayi a matsayin fanko tare da rashin kwarewa a aikin su.

A baya dai, wani sashe na jaridar, yace Atiku ake sa rai zai lashe zaben 2019 din, inda PDp tayi ta tsalle da murna da rahoton.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Mailfire view pixel