Hassan Rouhani ya sake lakuce ma Trump hanci kan takunkumi

Hassan Rouhani ya sake lakuce ma Trump hanci kan takunkumi

- Kasar Amurka bazata iya hana Iran kasuwancin mai ba.

- Kasar zatayi duk wani abu don ganin ta kare hanyoyin man ta

- Amurka bazata samu nasara akan karya tattalin arzikin kasar ta Iran ba

Hassan Rouhani ya sake lakuce ma Trump hanci kan takunkumi

Hassan Rouhani ya sake lakuce ma Trump hanci kan takunkumi
Source: UGC

A ranar Talata ne Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya bayyana cewa kasar Amurka bazata iya hana kasar sa kasuwancin mai ba.

Rouhani ya kara da cewa sun rufe duk wasu hanyoyin fitar da man don samun kariya.

Kasar ta Amurka ta sanyawa Iran doka inda take neman haramtawa kasar kasuwancin mai.

DUBA WANNAN: Yan siyasa su kai zuciya nesa kan 2019

A bangaren Rouhani yace kasar Amurka sunsan suna kasuwancin mai kuma bazasu iya hanasu ba.

An samu hargitsi ne a tsakanin kasashen Biyu bayan Shugaban kasar Amurka Donald Trump yaki amincewa da wani sulhu akan makamin nuclear sannan ya kara sanyawa kasar doka.

Ya kara d cewa kasar ta Amurka bazata taba samun nasarar karya tattalin arzikin Iran ba.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Mailfire view pixel