Gwamnonin APC 4 na shirin barin jam’iyyar zuwa AA - Kungiya

Gwamnonin APC 4 na shirin barin jam’iyyar zuwa AA - Kungiya

Kungiyar mabiya bayan APC reshen jihar Ondo wato Ondo APC Solidarity Group ta yi zargin cewa gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) hudu da wani minista, da tsohon babban jami’in jam’iyyar na shirin komawa jam’iyyar Action Alliance (AA) kafin zaben 2019.

Kungiyar ta yi zargin ne a ranar Talata, 4 ga watan Disamba yayin zantawa da yan jarida a hedkwatar APC da ke Abuja.

Jagoran kungiyar, Gbenga Bojuwomi da sakataren kungiyar na kasa, Alhaji Ibrahim Sikiru, wanda suka yi jawabi ga manema labarai sun ambaci sunan Gwamna Rotimi Akeredolu a matsayin shugaban jiga-jigan jam’iyyar da ke shirin sauya sheka.

Gwamnonin APC 4 na shirin barin jam’iyyar zuwa AA - Kungiya

Gwamnonin APC 4 na shirin barin jam’iyyar zuwa AA - Kungiya
Source: Facebook

Sauran yan kungiyar sune Gwamna Kayode fayemi, Rochas Okorocha, da kuma ibikunle Amosun.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kakakin APC a Imo ya yi murabus

Kungiyar ta kuma ambaci suan ministan ayyuka, wutar lantarki da gine-gine, Babatunde Fashola da wani tsohon mai ba APC shawara kan doka, Alhaji Muiz Banire a cikin shirin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel