Satar shanu: Gwamna Yari ya biya N10m don karbar bindigogi kirar AK-47 guda 10

Satar shanu: Gwamna Yari ya biya N10m don karbar bindigogi kirar AK-47 guda 10

- Gwamna Abdulaziz Yari ya ce bindigogi kirar AK-47 guda 10 ne gwamnatin jihar ta karba da aka kwato daga hannun barayin shanu akan N10m

- A watan Nuwambar wannan shekarar ne Yari ya bullo da wani tsaro, inda duk wanda ya gano bindiga kirar AK-47 daga barayin shanu, zai samu kyautar N1m

- Ya zargi kaka dokar ta baci a jihar Zamfara dangane da satar shanu, yana mai cewa ba jihar kadai bane ke fuskantar matsalolin tsaro ba

Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya ce bindigogi kirar AK-47 guda 10 ne gwamnatin jihar ta karba da aka kwato daga hannun barayin shanu a jihar biyo bayan bullo da tsarin biyan N1m akan duk wanda ya ajiye bindigarsa ko ya gano bindiga kirar AK-47.

A watan Nuwambar wannan shekarar ne Yari ya bullo da tsarin, inda duk wanda ya gano bindiga kirar AK-47 daga barayin shanu, zai samu kyautar N1m.

Da yake jawabi ga manema labarai a gidan fadar shugaban kasa, jim kadan bayan taro da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya ce zuwa yanzu an kwato bindigogi kirar AK-47 daga hannun barayin shanu.

KARANTA WANNAN: Cin amana: Mutumin da ya damfari tsohuwar budurwasa N5m ya gurfana gaban kotu

Satar shanu: Gwamna Yari ya biya N10m don karbar bindigogi kirar AK-47 guda 10

Satar shanu: Gwamna Yari ya biya N10m don karbar bindigogi kirar AK-47 guda 10
Source: Depositphotos

Yari, wanda shine shugaban kungiyar gwamnoni na kasa, ya ce akwai masu rike da sarautun gargajiya da dama da suke da hannu a satar shanu. A makon da ya gabata, gwamnatin jihar ta sauke rawanin wasu masu rike da sarautu guda 7.

Ya zargi kaka dokar ta baci a jihar Zamfara dangane da satar shanu, yana mai cewa ba jihar kadai bane ke fuskantar matsalolin tsaro ba.

"Shin ba a kashe jami'an tsaro a wurare daban daban a kasar, ko a Zamfara ne kawai ake yi? Me ya sa ba a kakaba dokar ta baci a wadancan wurare ba sai Zamfara kawai?" a tambayar Yari.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel