Zaben 2019: Ba maganar a mutu ko ayi rai bai ne wajen Buhari – Onyeama

Zaben 2019: Ba maganar a mutu ko ayi rai bai ne wajen Buhari – Onyeama

Mun ji labari cewa Ministan harkokin waje na Najeriya, Mista Geoffrey Onyeama ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai amince da duk yadda sakamakon zaben 2019 ya kama a Najeriya.

Zaben 2019: Ba maganar a mutu ko ayi rai bai ne wajen Buhari – Onyeama

Geofrey Onyeama yace Buhari zai amince da sakamakon zaben 2019
Source: Depositphotos

Geoffrey Onyeama ya bayyana wannan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai kwanan nan. Ministan na harkokin wajen Kasar yake cewa abin da ya fi damun Shugaba Buhari shi ne a ba kowa dama ya wanke allon sa.

Ministan ya tabbatar da cewa Shugaba Buhari a shirya yake ya gudanar da zabe nagari a 2019 wanda kuri’un kowa za su yi tasiri a Kasar. Ministan yace Shugaban kasar bai dauki maganar zaben wani abin a mutu ko ayi rai ba.

KU KARANTA: Buhari ba zai iya gyara Kasar nan cikin shekaru 4 ba – Tinubu

Onyeama ya kara da cewa ganin irin gwagwarmayar da Shugaba Buhari ya sha a zabukan Kasar da aka yi a baya, zai bada damar a gudanar da zabe na adalci a shekara mai zuwa. Oyeama yace Buhari zai yi wa Afrika abin a-zo-a-gani.

Ministan ya bayyana yadda Shugaba Buhari ya rika aika sa zuwa Kasashen Afrika irin su Guinea Bissau, Mali da Kasar Gambia domin ganin an yi zabe na kwarai. Onyeama yace don haka a shirya Gwamnati ta ke tayi abin kwarai a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel