Cin amana: Mutumin da ya damfari tsohuwar budurwasa N5m ya gurfana gaban kotu

Cin amana: Mutumin da ya damfari tsohuwar budurwasa N5m ya gurfana gaban kotu

- An gurfanar da Gbeminiyi Babajidde, mai shekaru 35 a gaban kotun lardi ta Ikeja, sakamakon damfarar tsohuwar masoyiyarsa N5m

- Wadannan laifuka da ake tuhumar wanda ake zargin sun ci karo da sashe na 287, 314 da 411 kundin dokar ta'addanci na Legas 2015, (wanda aka sabunta)

- Sai dai, wanda ake zargin, ya ce sam bai aikata wannan laifi da ake ikirarin ya aikata ba. Haka zalika, kotu ta bayar da belinsa akan kudi N250, 000

Sakamakon damfarar tsohuwar masoyiyarsa N5m da sunan zai sanya jari a wani kasuwanci, a ranar Talata ne aka gurfanar da tsohon jami'in sayar da gidaje, Gbeminiyi Babajidde, mai shekaru 35 a gaban kotun lardi ta Ikeja.

Wanda ake zargin, wanda ke zaune a gida mai lamba 10, titin Bolarinwa, Kajola, Ibadan, na fuskantar tuhuma kan aikata laifuka 2 na damfara da sata.

Jami'i mai shigar da kara, Sajen Michael Unah, ya shaidawa kotun cewa wanda ake zargin ya karbi N5m daga hannun tsohuwar budurwasa, Oluwaseun Giwa, da sunan zai taimaka mata wajen sanya jari a wani kasuwanci.

KARANTA WANNAN: Tsarin Allah: Tsohon minista da kakakin majalisa sun sha da kyar a wani harin bangar siyasa

Cin amana: Mutumin da ya damfari tsohuwar budurwasa N5m ya gurfana gaban kotu

Cin amana: Mutumin da ya damfari tsohuwar budurwasa N5m ya gurfana gaban kotu
Source: Depositphotos

Unah ya shaidawa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a tsakanin 2014 da 2016, a garin Surulere, Legas.

Ya ce tsohuwar budurwar mutumin, ta turawa masa N5m a asusun bankinsa, da nufin ya ajiye mata, wanda tayi nufin bude babban kantin sayar da kayayyaki da kudin.

"Wanda ake zargin ya juyar da kudin zuwa mallakinsa ba tare da sanin ita mai kudin ba, bayan da suka warware alakar soyayyar da ke tsakaninsu. Haka zalika duk wani yunkuri da akayi don ganin kudin sun fita daga wajensa abu yaci tura, har takai wanda ake zargin yana yi wa matar barazana idan har ta kara tambayarsa kudinta to zataga abunda zai same ta," a cewarsa.

Sai dai, wanda ake zargin, ya ce sam bai aikata wannan laifi da ake ikirarin ya aikata ba.

Babban mai shari'a na kotun lardin, Mr. A. A Fashola ya bayar da belin wanda ake zargin akan kudi N250, 000, tare da wakilai guda biyu.

Wadannan laifuka da ake tuhumar wanda ake zargin sun ci karo da sashe na 287, 314 da 411 na kundin laifuka na Legas 2015, (wanda aka sabunta). Kuma hukuncinsa shekaru 7 a gidan kaso sakamakon sata (sashe na 287) , da kuma shekaru 15 a gidan kaso sakamakon damfara ta hanyar karya (sashe na 314).

Mai shari'ar ya dage sauraron karar har sai 30 ga watan Janairu, 2019.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel