Likitoci sun kaddamar da yajin aiki, marasa lafiya sun shiga mawuyacin hali

Likitoci sun kaddamar da yajin aiki, marasa lafiya sun shiga mawuyacin hali

Biyo bayan yajin aikin da kungiyar likitocin Najeriya matsakaita reshen babbar asibitin koyarwa na jami’ar jahar Enugu ta kaddamar a ranar 28 ga watan Nuwamba, marasa lafiya da wadanda aka kwantar a asibitin sun fada mawuyacin hali.

Legit.com ta ruwaito ko a ranar Talata 4 ga watan Disamba wasu marasa lafiya dake da iko sun fice daga dakunan da aka basu zuwa wasu asibitocin da zasu samu kulawa, musamman asibitocin kudi.

KU KARANTA: Ashsha! Motar daukan kaya ta kufce ma direba, ta tattake mutum 10 har lahira

Likitoci sun kaddamar da yajin aiki, marasa lafiya sun shiga mawuyacin hali

Asibitin
Source: UGC

Wata babbar jami’ar kiwon lafiya, Nurse, data nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa marasa lafiyan sun sauya asibiti ne sakamakakon manyan likitocin dake asibitin ba zasu iya kulawa da dukkanin marasa lafiyan ba, amma wadanda asibitin na kulawa da masu bukatar kulawar gagga.

A bangaren kananan yara kuwa, yara biyu kadai aka bari a sashin saboda tsananin mawuyacin halin da suke ciki wanda har ta kai gas a musu numfashi ake yi, yayin da bangaren kulawa da marasa lafiyan kashi take dauke da yan tsirarun marasa lafiya.

Shugaban kungiyar Likitocin Najeriya reshen jahar Enugu, Dakta Ike Okwesili ya bayyana tasirin yajin aikin a matsayin mai muni, inda yace matakin ya jefa marasa lafiya cikin halin rashin sanin matabbata

Likita Okwesili ya kara da cewa yayi iya bakin kokarinsa wajen ganin ya tattauna da shuwagabannin kungiyar likitoci matsakaita da suka shiga yajin aikin tare da masu ruwa da tsaki don hana faruwar yajin aikin, amma hakarsa bata cimma ruwa.

A cewar shugaban likitocin, gwamnati ce ta gagara yi ma wadancan likitoci adalci, inda yace gwamnatin jahar Enugu bata biyan likitoci matsakaita dake babban asibitin koyarwa na jami’ar Enugu,ESUTH, wani muhimmin alawus, amma kuma tana biyan likitocin dake karkashin ma’aikatan kiwon lafiya na jahar.

Kuma duk kokarin da yayi wajen ganin an biya likitocin hakkin nasu yaci tura, sakamakon gwamnatin jahar Enugu ta ki yarda ta matsa daga matsayin da ta dauka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel