An yi ram da wani Fasto da laifin damfarar Bayin Allah a Legas

An yi ram da wani Fasto da laifin damfarar Bayin Allah a Legas

- Wani Fasto ya shiga hannun Hukuma da laifin damfarar Mabiyan sa

- Yanzu Alkalin Kotu bada belin wannan Fasto a kan kudi N200, 000

An yi ram da wani Fasto da laifin damfarar Bayin Allah a Legas

Wani Fasto a Legas ya gurfana a gaban Kotu da laifin damfara
Source: Depositphotos

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa wani Fasto mai suna Micheal Udom na cocin Pinnacle of Praise da ke Legas ya shiga hannun Hukuma a dalilin zargin sa da laifin damfarar Jama’a gudumuwar da su ke badawa.

Fasto Michael Udom wanda ke da mabiya a Legas ya gurfana a gaban Alkali mai shari’a A. A. Fashola na Kotun Majistaren da ke Garin Ikeja inda aka zargin sa da damfarar wasu Bayin Allah kudi har Naira Miliyan 1.5.

KU KARANTA: Sanatoci za su binciki Biliyan 23 da aka kashe wajen wani rububben aiki a Najeriya

Ana zargin wannan faston kawai din mai shekaru 52 a Duniya da karbar wannan kudi daga hannun Sylvia Nnamdi da kuma Alfred Olugbenga. Wani Jami’in ‘Yan Sanda Michael Unah shi ne ya bayyanawa Kotu wannan.

Yanzu dai Alkali ya bada belin wannan mutumi kan kudi N200, 000 tare da ba Kotu jingina. Laifuffukan da ake zargin wannan Fasto da shi sun sabawa dokokin Jihar Legas. Yanzu dai an dage shari’ar sai farkon 2019.

Idan har an samu wannan Malami da laifi ana iya daure sa na tsawon shekaru 15 a gidan yari. Ana karar Faston da laifin karya da damfara da kuma satar kudi. Yanzu dai Kotu ta nemi Faston ya kawo mutane 2 su tsaya masa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel