Kwamitin Shettima na yunkurin sasanta APC a kudu maso yamma, sun gana da Osinbajo

Kwamitin Shettima na yunkurin sasanta APC a kudu maso yamma, sun gana da Osinbajo

An kokarin hada kan ‘ya’yan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a kudu maso yamma inda kwamitin sulhu karkashin jagorancin gwamnan jihar Borno, Alhaji Kashim Shettima suka fara ganawa da mataimakn shugaban kasa Yemi Osinbajo.

A wani jawabi daga kakakin Shettima, Mallam Isa Gusau, yace ganawar na daga cikin tattaunawa tare da jin koke-koke daga shugabanni da mambobin APC a kudu maso yamma.

Ya bayyana cewa mataimakin shugaban kasar ya bayar da jawabin abunda shi ya fahimta akan lamarin a jihohi shida na Lagos, Ekiti, Ogun, Ondo, Osun da kuma Oyo da kuma mafita.

Kwamitin Shettima na yunkurin sasanta APC a kudu maso yamma, sun gana da Osinbajo

Kwamitin Shettima na yunkurin sasanta APC a kudu maso yamma, sun gana da Osinbajo
Source: UGC

Hadimin gwamnan ya kuma ce Shettima da sauran mambobin kwamitin sulhun da APC ta shirya za su sasanta fusatattun mambobin jam’iyyar a yankin kudu maso yamma sun je fadar shugaban kasa domin tutubar Osinbajo.

KU KARANTA KUMA: Kannywood: Rahama Sadau ta yi murnar samun yawan mabiya miliyan 1 a Instagram

Gusau yace sauran mambobin kwamitin sun hada da Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasru El-Rufai, tsohon mataimakin Gwamnan jihar Ekiti, Farfesa Modupe Adelabu; darakta janar na NIMASA, Dr. Dakuku Peterside da kuma Sa’ida Sa’ad Bugaje.

A gobe ne ake sanya ran kwamitin zata gayyaci fusatattum mambobin jam’iyyar daga jihohi shda domin jin ta bakinsu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel