Kada ku zabe ni idan ba za ku zabi Buhari ba – Candido

Kada ku zabe ni idan ba za ku zabi Buhari ba – Candido

Shugaban yankin birnin Abuja, Hon Abdullahi Adamu Candido, ya yi kira ga magoya bayansa da kada su zabe shi, idan har sun san cewa ba za su zabi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba a zaben 2019.

Da yake Magana a wani taro na ‘Next Chapter’, wanda shine taken zaben sa na 2019, Candido ya bayyana cewa Shugaba Buhari yayi kokari sosai a shekaru uku da rabid a yayi yana mulki kuma ya cancanci tazarce.

Kada ku zabe ni idan ba za ku zabi Buhari ba – Candido

Kada ku zabe ni idan ba za ku zabi Buhari ba – Candido
Source: Twitter

Ya kara da cewa gwamnatin jam’iyyar All Progressives Congress (APC)- karkashin jagorancin Shugaba Buhari ta samu nasarori mai yawa wanda gwamnatocin baya ba su samu ba.

Ya kuma bayyana cewa wahalar rayuwar da ake fuskanta a kasar a yanzu ba yin gwamnati mai ci bane, sai dai barnar da gwamnatocin baya suka shafe shekaru 16 suna yi.

Daga karshe ya bayyana cewa a shekarun da yayi yana shugabanci a AMAC ya samu tarin nasarori da ayyukan ci gaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel