Buhari ne zabin mutanen yankin kudu maso yamma - Jigo a APC

Buhari ne zabin mutanen yankin kudu maso yamma - Jigo a APC

- A jiya ne wata kungiyar Yarabawa ta sanar da cewa ta cimma matsayar zaben Atiku Abubakar a 2019 saboda ya yi alkawarin zai sauya tsarin fasalin rabon arzikin kasa

- Kungiyar ta fitar da sanarwar ne a cikin sakon bayan taron da ta gudanar a Muson Centre da ke Onikan a jihar Legas

- Sai dai a yanzu kuma wani jigo a jam'iyyar APC daga yankin na Yarabawa ya ce ayi watsi da wancan batun domin Buhari ne dan takarar da Yarabawa suka tare da shi

Wani jigon jam'iyyar APC a jihar Legas, Chief Tajudeen Olusi ya yi watsi da goyon bayan da wasu jiga-jigan yankin Kudu maso yamma suka yiwa Atiku Abubakar inda ya ce Allah ne ya aiko mana da Shugaba Muhammadu Buhari kuma har yanzu shine zabin al'ummar yankin Yarabawa a zaben 2019.

Cif Olusi ya ce nan gaba yankin za ta bayyana matsayar ta game da dan takarar da za ta zaba a 2019.

Buhari ne zabin mutanen yankin kudu maso yamma - Jigo a APC

Buhari ne zabin mutanen yankin kudu maso yamma - Jigo a APC
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Shugabanin kabilar Yarabawa sun goyi bayan Atiku

A yayin hirar da ya yi da Daily Trust, ya ce, "A lokacin da ya dace, al'ummar Yarabawa za suyi magana, amma ina son in tabbatar maka cewa sanin da na yiwa al'ummar Yarabawa da suke zaune a Kudu maso yammacin Najeriya, muna da dan takarar da muke goyon baya kuma shine Muhammadu Buhari wadda Allah ya aiko mana zuwa kasar."

Da aka masa tambaya a kan dan takarar da yankin Kudu maso yamma za ta zaba, Kakakin kungiyar Afenifere, Mr Yinka Odumakin ya ce kungiyar za ta zabi dan takarar da ke da niyyar sauya tsarin rabon tattalin arzikin kasa ne.

Ya kara da cewa kungiyar tana hadin gwiwa da sauran kungiyoyin kudu wadda suka dade suna neman a sake fasalin tsarin rabon arzikin Najeriya.

A halin yanzu, dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar shine ya fi mayar da hankali a kan batun sauya fasalin rabon arzikin kasar, Atiku ya bayyana cewa zai iya bawa jihohin da ke samar da man fetur ikon karbar ribar da ake samu daga man fetur din ila iya zai sanya musu haraji idan ya yi nasarar lashe zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel