Yanzu Yanzu: Kakakin APC a Imo ya yi murabus

Yanzu Yanzu: Kakakin APC a Imo ya yi murabus

Rikicin da ke faruwa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Imo ya yi kamari yayinda kakakin jam’iyyar a jihar, Mista Jones Onwuasoanya ya yi murabus.

Onwuasoanya, wanda ya bayyana APC a matsayin kungiyar asiri ba na siyasa ba, ya zargi shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, da lalata jam’iyyar, cewa shugaban jam’iyyar ya sanya kokwanto a zukatan mutane da dama.

Yanzu Yanzu: Kakakin APC a Imo ya yi murabus

Yanzu Yanzu: Kakakin APC a Imo ya yi murabus
Source: Facebook

Ya bayyana cewa Oshiomhole ya take hakkin yan jam’iyya, doka da kuma tsarin damokradiyya, inda ya fi son ya farantawa na kewaye da shi tare da son zuciya da kuma tallata mulki.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Mutane da dama sun mutu yayinda rikici ya barke a garuruwan Cross River

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, yayi alkawarin kin bada goyon bayan shi ga Dan takarar shugabancin gwamnan jihar.

Mista Amosun makusanci ne ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, yayi alkawarin aiki tukuru don ganin zarcewar shugabancin shugaban kasar.

Yace ba zai bar jam'iyyar APC ba kuma zai nemi kujerar sanatan jihar ta tsakiya a karkashin inuwar jam'iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel