Hana sa hijabi: Iyayen dalibai sun maka makarantar sakandire na jami'ar Ibadan a kotu

Hana sa hijabi: Iyayen dalibai sun maka makarantar sakandire na jami'ar Ibadan a kotu

Wasu iyayen dalibai mata na International School, Ibadan (ISI) sun shigar da mahukunta makarantar kara a kotu saboda hana 'yayansu sanya hijabi yayin da za su tafi makarantar.

The Cable ta ruwaito cewa wadanda suka shigar da karar a babban kotun Oyo da ke Ibadan sun hada da Taofeek Yekinni, Idris Badiru, Sikiru Babarinde, Muideen Akerele da wasu mutane 10.

A cikin sammacin da aka aike wa mahukuntar makarantar, lauyan wadanda suka shigar da karan, Lateef Fagbemi (SAN) ya bukaci kotun ta zartar da cewa hana dalibai mata musulmi sanya hijabi da ISI tayi kuskure ne kuma ya sabawa kundin tsarin kasa.

Hijabi: Iyayen yara sun maka makarantar sakandire na jami'ar Ibadan a kotu

Hijabi: Iyayen yara sun maka makarantar sakandire na jami'ar Ibadan a kotu
Source: UGC

DUBA WANNAN: Ma'aikatan kananan hukumomin Zamfara ne ma fi koma baya a albashi

Fagbemi ya ce matakin da mahukunta ISI suka dauka ya keta hakkin wadanda suka shigar da karar na damar yin addininsu da samun ilimi kamar yadda sashi na 38 (1)(a) da 42(1)(a) na kundin tsarin mulkin Najeriya ya basu dama.

Ya ce kule daliban ko kuma cin zarafinsu da mahukuntar makarantar ko wakilansu su kayi saboda saka hijabin ya saba hakkin su na 'yan adam.

Ya bukaci kotun ta zartar da hukuncin da zai hana mahukuntar makarantar da wakilansu daukan wani mataki na yin katsalandan cikin yadda daliban su kayi niyyar amfani da damar da kundin tsarin mulkin kasa ta basu na yin addininsu.

Za a fara sauraron shari'ar a ranar 21 ga watan Disamban 2018 a gaban mai shari'a Ladiran Akintola na babban kotun Ibadan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel