2019: PDP da sauran jam'iyyu zasu tarwatse, suna ji suna gani Buhari zai zarce - The Economist

2019: PDP da sauran jam'iyyu zasu tarwatse, suna ji suna gani Buhari zai zarce - The Economist

- Mujallar da ta sanu a duniya, Economist, ta yi hasashen cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sake lashe zaben shugaban kasa a 2019

- A cikin sabuwar mujallar da Economist ta wallafa, ta ce jam'iyyun adawa za su tarwatse kafin babban zaben 2019 don baiwa Buhari hanyar tazarce

- A fitowar sabuwar mujallar mai taken, "Duniya a 2019:, akwai yakinin cewa rikici da ta'addancin mayakan Boko Haram zai zo karshe

Shahararriyar mujallar ta duniya, Economist, ta ruwaito cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sake lashe zaben shugaban kasa a babban zabe na 2019 don bashi damar yin tazarce.

Wannan hasashe kamar gugar zana ne ga martanin da dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi, na cewar kafar watsa labaran wacce take da zama a Landan ta gaza cimma ka'idoji na adalci da dai-daito ta hanyar kaucewa nuna bangaranci.

A fitowar sabuwar mujallar mai taken, "Duniya a 2019:, akwai yakinin cewa rikici da ta'addancin mayakan Boko Haram zai zo karshe.

KARANTA WANNAN: Gwamnatina ba zata runtsa ba har sai ta kubutar da sauran 'yan matan Chibok - Buhari

2019: PDP da sauran jam'iyyu zasu tarwatse, suna ji suna gani Buhari zai zarce - The Economist

2019: PDP da sauran jam'iyyu zasu tarwatse, suna ji suna gani Buhari zai zarce - The Economist
Source: Depositphotos

Da take tsokaci kan kasar Nigeria, mujallar ta ce: "Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai lashe zabensa a karo na biyu a watan Fabreru, kasancewar gamayayyar jam'iyyun da suka hadu don adawa da shi (Buhari) zasu tarwatse kafin lokacin zabe.

"Duba da irin yadda tsarin siyasar demokaradiyya ke samun nakasu, yakin samun nasara a yaki da 'yan ta'addan Boko Haram na da rauni sosai a yankin Arewa, da kuma farfado da yakin Niger Delta, da ma kwantar da tarzomar masu fafutukar kafa kasar Biafra."

A baya bayan nan, Legit ta ruwaito maku cewa dan takarar shugaban kasa krkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana rahoton mujallar The Economist da ke Landan na goyon bayan takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC a matsayin nuna bangaranci da kuma tsomahannu a harkokin siyasa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel