Gwamnatina ba zata runtsa ba har sai ta kubutar da sauran 'yan matan Chibok - Buhari

Gwamnatina ba zata runtsa ba har sai ta kubutar da sauran 'yan matan Chibok - Buhari

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin gwamnatinsa ba zata runtsa ba har sai sauran 'yan matakn da aka sace sun kubuta

- Shugaban kasar ya bayar da tabbacin cewa 'yan matan Chibok da aka sace da ma wadanda aka yi garkuwa da su, za su ci gaba da zama kan gaba a tunanin gwamnatin tarayya

- Ya kuma bayyana cewa kofa a bude take ga duk wadanda suke ganin za su iya tallafawa wajen gubuto da sauran 'yan matan da aka sace

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa gwamnatinsa ba zata huta ba har sai ta kubuto da sauran 'yan mata Chibok da 'yan ta'addan Boko Haram suka sace a watan Afrelu, 2014.

Ya jaddada wannan yunkurin nasa a wata tattaunawa da yayi da shugaban kasar Swiss, Alain Berset, a ci gaba da taron majar taron majalisar dinkin duniya na canjin yanayi, COP24, da ake gudanarwa a birnin Katowice, Poland, a ranar Litinin, 3 ga watan Disamba.

Legit.ng ta tattara rahoto cewa wannan alwashin da shugaban kasar ya yi, na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga babban mai tallafa masa ta fuskar watsa labarai, Garba Shehu.

KARANTA WANNAN: Mubayi'a ga takarar Atiku ta jawo rabuwar kawuna a tsakanin shuwagabannin Yoruba

Gwamnatina ba zata runtsa ba har sai ta kubutar da sauran 'yan matan Chibok - Buhari

Gwamnatina ba zata runtsa ba har sai ta kubutar da sauran 'yan matan Chibok - Buhari
Source: Depositphotos

Shugaban kasar ya godewa takwaransa na kasar Swiss bisa yunkurin gwamnatin kasarsa na zama a matsayin mai shiga tsakani wajen kubutar da wasu 'yan matan Chibok a kwanakin baya.

Ya kuma kara jaddadawa Berset cewa batu kan kubutar da sauran 'yan matan na Chibok da ma duk wadanda aka yi garkuwa da su, zai ci gaba da zama kan gaba a kowanne tunani na gwamnatin tarayya.

Shuwagabannin kasashen guda biyu sun tattauna hanyoyi kan yadda za a kubutar da 'yan matan, ta hanyar la'akari da yadda aka bi har aka kubutar da wasu 'yan matan a kwanakin baya.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel