Masarautar Igbo ta nada wa Shugaba Buhari sarauta

Masarautar Igbo ta nada wa Shugaba Buhari sarauta

Masarautar Umunneochi da ke karamar hukumar Isukwuato Umunneochi na jihar Abia ta nada wa Shugaba Kasa Muhammadu Buhari sarautar IKE-OGU NDIGBO.

Mai martaba Okechukwu Chukwuji, Logu 1 na Amuda Kingdom ya bayyana cewa an nada wa shugaban kasar sarautar ne saboda jajircewarsa wajen watsa ayyukan cigaba a yankin kudu maso gabas, musamman a karamar hukumar Isukwuato Umunneochi.

Masarautar Igbo ta nada wa Shugaba Buhari sarauta

Masarautar Igbo ta nada wa Shugaba Buhari sarauta
Source: Depositphotos

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Gaduje ne ya karbi sarautar a madadin shugaban kasar a jihar Abia, inda ya je a matsayin shugaban kwamitin sulhu na APC a yankin arewa maso gabas.

KU KARANTA KUMA: Babu wanda Atiku ya fada ma cewa ya karbi bizan Amurka – Jami’in kungiyar kamfen

Sarkin yayi amfani da damar ziyarar da kwamitin suka kai jihar wajen bayar da sarautar domin a mgabatar da shi ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

A wani lamari na daban, mun ji cewa Sanata Oluremi Tinubu wanda ta ke wakiltar Legas ta tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya tayi magana game da batun Majalisar Tarayya da Gwamnatin Shugban Kasa Muhammadu Buhari da kuma babban zaben da za ayi a 2019.

Oluremi Tinubu tayi kira ga mutane su sake marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari dama a zaben 2019. ‘Yar Majalisar tace Shugaban kasa Buhari ba zai iya gyara Najeriya a cikin shekaru 4 tal ba don haka ya kamata ya zarce.

Remi Tinubu ta tabbatar da cewa za ta sake neman kujerar Sanata a karo na uku. Tinubu tace za tayi takarar ne domin Dattawan Legas sun yi na’am da wakilcin ta. Sanatar tace Buhari ba zai kuma samun matsala da Majalisa a 2019 ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel