Yanzu-yanzu: Ma'aikatan majalisar dokoki sun hana majalisa zama, suna zanga-zanga

Yanzu-yanzu: Ma'aikatan majalisar dokoki sun hana majalisa zama, suna zanga-zanga

Ma'aikatan majalisan dokokin tarayya da ke birnin tarayya Abuja suna gudanar da zanga-zanga da safiyar yau Talata, 5 ga watan Disamba, 2018.

Ma'aikatan sun bayyana cewa suna bin albashi tun shekarar 2010 kuma har yanzu ba'a biyasu ba. Kana an karkatar da kudaden da ya kamata a basu domin horo da kara fasaha.

Ma'aikatan suna rike da manyan takardu sun cewa "Babu albashi, babu zama"

Yanzu-yanzu: Ma'aikatan majalisar dokoki sun hana majalisa zama, suna zanga-zanga

Yanzu-yanzu: Ma'aikatan majalisar dokoki sun hana majalisa zama, suna zanga-zanga
Source: Twitter

Kokarin da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, yayi domin kwantar da kuran ma’aikatan majalisar masu zanga-zanga ya sha kasa. Ma’aikatan sun yi banza da shi kuma sun koreshi.

Bugu da kari, wata mota kirar Toyota Coaster ta iso majalisar cike da mambobin kungiyar kwadagon Najeriya NLC domin karawa ma’aikatan karfin gwiwa.

Ma’aikatan sun mamaye zauren majalisar kuma sun hana yan majalisa shiga.

Bidiyo:

Zamu kawo muku cikakken rahoton...

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel