Maryam Sanda: Shekara daya bayan kisan Bilyaminu, an nemi mai bada shaida an rasa a kotu

Maryam Sanda: Shekara daya bayan kisan Bilyaminu, an nemi mai bada shaida an rasa a kotu

Rashin mai bada shaida, Hussein Okpetu, a kotu ya hana karar Maryam Sanda da ake zargi da kisan mijinta cigaba a kotu.

Mr Hussein Okpetu ya kasance mutum na shida da zai bada shaida a kotu kan yadda aka kasha Bilyaminu.

Ana tuhumar Maryam Sanda ne da kisan Bilyaminu Bello, dan tsohon shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Hallitu Bello. An gurfanar da ita ne tare da mahaifiyarta, Maimuna Aliyu; dan uwanta, Aliyu Sanda; da mai aikin gidansu, Sadiya Aminu.

A ranan Litinin, lauyan gwamnati, Fidelis Ogbegbe, ya gabatar da Josephine Onyentu, domin bada shaida a kotu sakamakon rashin ganin Mr Hussein Okpetu.

Lauyan ya bayyana cewa an kawo wata daban ne saboda hukumar yan sandan Najeriya ta mayar da Hussein Okpetu jihar Ondo kuma aka maye girbinsa da Mrs Onyetu, tunda mamba ce a kwamitin binciken.

KU KARANTA: APC ta mayarwa Buhari martani kan Koran mambobin jam’iyyar

Amma lauyan Maryam Sanda, Olusegun Jolawa, ya ce bai dade ba a gabatar da mai bada shaida wanda babu sunansa cikin masu bada shaida.

Mr Jolawo ya ambaci sashe 379 na kundin tsarin mulki wanda yace wajibi ne duk mai bada shaida ya gabatar da hujja kafin bada shaida.

Lauyan gwamnati Mr Ogbegbe yace tunda lauyan gwamnati bai amince wata ta bada hujja a madadin Hussein Okpetu ba, yana bukatar okaci domin tattaunawa da shi kan yadda zai halarci zaman kotu a ranan da alkali ya bada.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel