Mubayi'a ga takarar Atiku ta jawo rabuwar kawuna a tsakanin shuwagabannin Yarabawa

Mubayi'a ga takarar Atiku ta jawo rabuwar kawuna a tsakanin shuwagabannin Yarabawa

- An samu rabuwar kawuna a tsakanin shuwagabannin al'ummar Yoruba, dangane da mubayi'a ga Atiku Abubakar, a matsayin dan takarsu na shugaban kasa a zaben 2019

- Tsohon sakataren jam'iyyar PDP na kasa, Dr. Remi Akitoye, ya gabatar da wannan kuduri na yin mubayi'a ga Atiku a wajen wani taro na shuwagabannin shiyyar Kudu maso Yamma

- Sai dai, ba a nan gizo yake tasa sakarba, domin kuwa, shuwagabannin APC sun bijirewa wannan taro, wanda hakan ya kawo rabuwar kawuna a tsakanin shuwagabannin

An samu rabuwar kawuna a tsakanin shuwagabannin al'ummar Yoruba a ranar Litinin, dangane da mubayi'a ga dan takarar PDP, Atiku Abubakar, a matsayin dan takarsu na shugaban kasa a shiyyar a babban zaben 2019.

Wasu daga cikin shuwagbannin Yoruba, karkashin inuwar kungiyar Kudu maso Yamma, kungiyar hadakar kungiyoyin fararen hula da kuma kungiyoyin sa kai, a karshen wani taro da suka gudanar a Legas, sun yanke shawarar amincewa da Atiku Abubakar a matsayin dan takarsu na shugaban kasa.

Taron mai taken "2019: Kudu maso Yamma zata fayyace amtsayarta", ya samu halartar shuwagabannin PDP da kuma shuwagabannin Afenifere, dama wasu daga cikin jiga jigan jam'iyyar ADP.

KARANTA WANNAN: A shirye nake mu fafata a taron muhawarar shugaban kasa - Atiku ya shaidawa Buhari

Mubayi'a ga takarar Atiku ta jawo rabuwar kawuna a tsakanin shuwagabannin Yoruba

Mubayi'a ga takarar Atiku ta jawo rabuwar kawuna a tsakanin shuwagabannin Yoruba
Source: Facebook

Sai dai, ba a nan gizo yake tasa sakarba, domin kuwa, shuwagabannin APC sun bijirewa wannan taro, wanda hakan ya kawo rabuwar kawuna a tsakanin shuwagabannin al'ummar Yoruba, don kuwa ba dukkannsu bane suka amince da wannan mubayi'a ga takarar Atiku.

Tsohon sakataren jam'iyyar PDP na kasa, Dr. Remi Akitoye, ya gabatar da wannan kuduri na yin mubayi'a ga Atiku a wajen taron.

Kungiyar ta cimma matsayar marawa Atiku baya saboda kudurinsa na sake fasalin kasar, inda ta jaddada cewar akwai rashin aldalci a yadda ake raba ikon shuwagabannin kasar, la'akari da cewa ana fifita wani bangare akan wani.

Taron ya samu halartar dan takarar gwamnan jihar Legas karkashin jam'iyyar PDP, Mr. Jimi Agbaje, da abokiyar takararsa, Mrs. Haleemat Busari; dan takarar gwamnan jihar karkashin ADP, Babatunde Gbadamosi; da kuma dan takarar gwamnan jihar Oyo karkashin PDP, Engr. Seyi Makinde.

Sauran sun hada da shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, Abiodun Olujimi, mataimakin shugaban PDP na kasa a shiyyar Kudu maso Yamma, Dr. Eddy Olafeso, tsohon sakataren jam'iyyar PDP na kasa, Chief Ebenezer Babatope, shugaban PDP na jihar Legas, Dr. Adegbola Dominic,da kuma shugaban ADP na jihar, Barr. Adewole Bolaji.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel