Yawan wadanda suka ajje Buhari don Atiku ya kai 59 ya zuwa yanzu

Yawan wadanda suka ajje Buhari don Atiku ya kai 59 ya zuwa yanzu

- Wasu kungiyoyi sun bar Buhari sun komawa Atiku

- Wadannan kungiyoyi sun hada da ma'aikatan tafiye tafiye,yan kasuwa da kuma yan kabu kabu(Okada)

- Sunce a karkashin mulkin Atiku suna da tabbbacin tattalin arziki zai dawo

Yawan wadanda suka ajje Buhari don Atiku ya kai 59 ya zuwa yanzu

Yawan wadanda suka ajje Buhari don Atiku ya kai 59 ya zuwa yanzu
Source: Twitter

Wasu kungiyoyi 59 dake goyan bayan mulkin Shugaban kasa Muhammad Buhari sunyi tawaye sun koma bayan Atiku Abubakar.

Shugaban kungiyar ta Grassroots Mobilisers Yusuf Musa Ardo ya bayyana canjin da sukayi a maimakon kungiyoyin 59 a ranar Litinin a Abuja.

Ardo ya bayyana dalilin su na barin goyawa shugaba Buhari baya suka komawa Atiku.

Yace ina farin cikin tsayawa yau a maimakon abokan aiki na na kungiyar mu wadda aka kafata a shekara ta 2015 don goyawa Buhari baya,wannan kungiya tana da 'ya'ya sama da Miliyan Biyar wadanda suka hada da yan kasuwa, ma'aikatan tafiye tafiye, 'yan kabu-kabu (Okada) da sauran su.

DUBA WANNAN: Osinbajo na zaman sirri da gwamna Yari kan babatunsa

A yau kasar mu tana fuskantar kalubale a bangaren tsaro,tattalin arziki da kuma ta'addanci.

Muna farin cikin bayyana muku cewa wannan kungiya tamu ta tattara komatsanta ta koma bayan Atiku Abubakar wanda yake neman kujerar Shugaban cin kasar nan a shekara ta 2019.

Ardo ya kara da cewa suna ta tabbacin idan Atiku ya samu wannan shugaban ci zai kawo karshen duk wadancan abubuwan daya lissafa a sama.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Mailfire view pixel