Jam'iyyu na so a dakatar da dokar zabe a 2019, lauyoyi sunyi fashin baqi

Jam'iyyu na so a dakatar da dokar zabe a 2019, lauyoyi sunyi fashin baqi

- Dokar zaben dai ta 2018 ce, wadda kuma wasu jam'iyyun bassu so ayi aiki da ita

- Majalisa ta mikawa shugaba Buhari dokar ya rattaba hannu

- Lauyoyi sunyi bayani kan lamarin

Jam'iyyu na so a dakatar da dokar zabe a 2019, lauyoyi sunyi fashin baqi
Jam'iyyu na so a dakatar da dokar zabe a 2019, lauyoyi sunyi fashin baqi
Source: UGC

Sabuwar dokar zabe da dole sai shugaba Buhri ya sanya hannu zata cika ayi aiki da ita a zabukan badi na uskantar kalubale, bayan da wasu jam'iyyu ke ganin kamata yayi a dakatar da aiki da ita sai dai ko a 2023, kuma sun garzaya kotu kan wannan bukata.

Lauyoyi sunyi magana akan hana shugaban kasa sa hannun akan sababbin dokokin zabe. A ranar litinin, jam'iyyu uku ne suka tambaya ko sababbin dokokin zaben bazasu shafin zabe Mai zuwa ba. An tura dokokin ne ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a 8 ga watan Nuwamba .

Lauyoyi sunyi magana akan karar da jam'iyyun siyasa suka ka don hana shugaban kasa Muhammadu Buhari sa hannu akan sababbin dokokin zabe da majalisar dattawa ta mika shi a watan Octoba.

Jam'iyyun siyasa uku ne a ranar litinin suka tunkari babban kotun tarayya don hana shugaban kasa saka hannun a dokokin yanzu.

DUBA WANNAN: Yawan kungiyoyin da suka bar Buhari don Atiku

Jam'iyyar APDA, APM da MRDD ne suka bukaci kotu da ta sanar cewa sababbin dokokin Baza su shafi zaben 2019 ba.

An tura sababbin dokokin ga Mista Buhari ne a ranar 8 ga watan Nuwamba bayan da majalisar dattawa ta gama duba su a watan Octoba.

Dokokin sun jawo hankulan masana shari'a da yan siyasa wadanda suka ce mahukuntan na iya amfani da sashi na 58, sakin layi na biyar na kundin tsarin mulkin kasa da yace zasu iya karbar dokokin Idan sukayi kwanaki 30 ba tare da yasa hannu ba sannan su maida su dokoki ba tare da sukar adawar shugaban kasar ba, inji Inebehe Effiong, Lauya kuma mai bada shawara ga wata jam'iyyar siyasa.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Online view pixel