APC ta mayarwa Buhari martani kan Koran mambobin jam’iyyar

APC ta mayarwa Buhari martani kan Koran mambobin jam’iyyar

Da yiwuwan uwar jam’iyyar All Progressives Congress APC za ta salami wasu mambobin jam’iyyar da suka kai karan uwar jam’iyyar kotu bisa ga sakamakon zaben fidda gwanin jam’iyyar.

Kwamitin gudanarwan jam’iyyar ta yi watsi da maganar Buhari da ya nuna rashin amincewarsa da wannan mataki.

A makon da ya gabata, Buhari ya bayyana cewa mambobin APC na da hakkin kai kara kotu kan sakamakon zaben fiida gwani.

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Cif Hillard Eta, ya bayyana matsayar jam’iyyar a wata hira da jaridar Sunday Punch.

Eta yace da yawa daga cikin mambobin jam’iyyar da suka kai kara kotu basuyi amfani dukkan matakan sulhu ba kafin zuwa kotu.

Ya ce jam’iyyar ba zata canza matsayarta ba akan wannan al’amari ba. Ya jaddada cewa zasu hukunta wadannan mambobi wanda zai hada da korarsu daga jam’iyyar.

Yace: “Ya kamata mu hada jawabin shugaban kasa da matsayar jam’iyar. Kundin tsarin mulkin jam’iyya ta ce wajibi ne mamba yayi amfani da dukkan matakan sulhu kafin kai kara kotu.”

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel