A hukunta yan Shi’a a matsayin yan ta’adda – Kungiyoyin fafutuka sunyi ittifaki

A hukunta yan Shi’a a matsayin yan ta’adda – Kungiyoyin fafutuka sunyi ittifaki

Domin kawo karshen rashin zaman lafiya ta hanyar zanga-zanga da tattaki, an yi ittifaki a taron kungiyoyin fafutukan Najeriya CSO da wasu masu ruwa da tsaki da ya gudana a Abuja cewa a hukunta shugabannin mabiya akidar Shi’a da mambobinsu matsayin yan ta’adda.

Wata takardar ittifakin da aka gabatar a karshen taron wanda Jonathan Audu, Abubakar Wakil Mohammad da Osita Egbuniwehe suka sanya hannu ya ce idan ba’a dau matakin gaggawa kan abubuwan da yan Shi’a ke yi ba, zasu iya zama babbar matsala nan gaba.

a taron, an tattauna abubuwan da suka faru a kwanakin kusan nan da suka shafi tsattsaurin ra’ayin addini da ta’addanci da kuma irin fito-na-fito da kungiyar mabiya akidar Shi’a ke yiwa jami’an tsaron Najeriya wanda yayi sanadiyar hasaran rayuka da dama.

A hukunta yan Shi’a a matsayin yan ta’adda – Kungiyoyin fafutuka sunyi ittifaki

A hukunta yan Shi’a a matsayin yan ta’adda – Kungiyoyin fafutuka sunyi ittifaki
Source: Facebook

A wannan taro, an kaddamar da wani littafi mai suna “Ta’addanci da daula: Kyakkyawan dubi cikin kungiyar mabiya addinin Shi’a” wanda Sunday Attah ya wallafa. Ya yi bayanin asalin Shi’a da irin kallon da sukewa gwamnatin Najeriya.

KU KARANTA: Rundunar sojin Najeriya na artabu da yan Boko Haram a MalamFatori - Ahmed Salika

Jama’ar da suka halarci taron sun bayyana cewa a karshen wannan shekara, mabiya akidar Shi’a sun yi iyakan kokarinsu wajen mayar da birnin tarayya Abuja hedkwatansu da sunan zanga-zangan neman sakin shugabansu, Ibrahim Zakzaky, wanda ake gurfanarwa a babban kotun Kaduna.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel