An yi walkiya: Yanzu Buhari ya san ainihin Mutanen da ke son sa – Remi Tinubu

An yi walkiya: Yanzu Buhari ya san ainihin Mutanen da ke son sa – Remi Tinubu

- Sanata Remi Tinubu tace yanzu Shugaba Buhari ya gane asalin wadanda ke tare da shi

- Babbar Sanatar ta nemi Jama’a su sake ba Gwamnatin APC ta Buhari dama a zaben 2019

An yi walkiya: Yanzu Buhari ya san ainihin Mutanen da ke son sa – Remi Tinubu

Tinubu tayi kira ga ‘Yan Najeriya su sake zaben Buhari a 2019
Source: UGC

Sanata Oluremi Tinubu wanda ta ke wakiltar Legas ta tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya tayi magana game da batun Majalisar Tarayya da Gwamnatin Shugban Kasa Muhammadu Buhari da kuma babban zaben da za ayi a 2019.

Oluremi Tinubu tayi kira ga mutane su sake marawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari dama a zaben 2019. ‘Yar Majalisar tace Shugaban kasa Buhari ba zai iya gyara Najeriya a cikin shekaru 4 tal ba don haka ya kamata ya zarce.

KU KARANTA: Atiku Abubakar ne ‘Dan takarar da zai yi maganin yunwa - Kwankwaso

Remi Tinubu ta tabbatar da cewa za ta sake neman kujerar Sanata a karo na uku. Tinubu tace za tayi takarar ne domin Dattawan Legas sun yi na’am da wakilcin ta. Sanatar tace Buhari ba zai kuma samun matsala da Majalisa a 2019 ba.

Mai dakin Jigon na Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ta kuma bayyana cewa yanzu kar-ta-san-kar domin kuwa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gane wadanda su ke tare da shi da masu neman kawo masa cikas a mulkin sa.

Tinubu tace a lokacin da Buhari ya karbi mulki, yayi ikirarin cewa kowa na sa ne, amma tace yanzu Shugaban kasar ya gane cewa ba kowa bane na sa. Sanata Tinubu ta na sa rai Buhari ba zai yi fama da ‘Yan adawa a Majalisa a 2019 ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel