An umurci Buratai da ya ci gaba da kasancewa a arewa maso gabas har sai yanayin tsaro ya inganta a yankin

An umurci Buratai da ya ci gaba da kasancewa a arewa maso gabas har sai yanayin tsaro ya inganta a yankin

Ministan tsaro, Mansur Dan Ali, ya umurci shugaban hafsan sojojin Najeriya Janar Tukur Buratai da ya ci gaba da kasancewa a yankin arewa maso gabashin kasar har sai yanayin tsaro ya inganta a yankin.

Hakan ya kasance daya daga cikin sabbin dabarun da kasar ta ke dauka dangane da yakin da take yi da yan ta'addan Boko Haram wadanda suka kara karfafa kai hare-hare kan jami'an tsaron kasar.

A kwanan nan ne dai yan ta'addan suka kai mumunan hari ka sansanin sojojin kasar da ke Borno wanda yayi sanadiyar mutuwar sojoji da dama.

An umurci Buratai da ya ci gaba da kasancewa a arewa maso gabas har sai yanayin tsaro ya inganta a yankin

An umurci Buratai da ya ci gaba da kasancewa a arewa maso gabas har sai yanayin tsaro ya inganta a yankin
Source: Depositphotos

Gwamnatin kuma ta ce za ta inganta walwalar sojin kasar, musamman wadanda ke fagen fama.

A wata sanarwa daga Kanal Tukur Gusau, kakakin ministan tsaro, ministan ya kuma bukaci babban kwamanda mai lura da runduna ta 8 ta sojin da ya mayar da hedikwatar sa zuwa Gusau babbar birnin jihar Zamfara daga jihar Sokoto mai makwabtaka.

KU KARANTA KUMA: Ya kamata Buhari ya fallasa wadanda su ka nemi kujerar sa tun kafin ya bar Duniya – Shehu Sani

An kuma bukaci Buratai da babban hafsan sojin kasa da su gudanar da sauye-sauye a rundunonin Delta Safe a yankin Naija Delta da operation lafiya dole a arewa maso gabas da kuma kakkabe Daji a jihar Zamfara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel