Ya kamata Buhari ya fallasa wadanda su ka nemi kujerar sa tun kafin ya bar Duniya – Shehu Sani

Ya kamata Buhari ya fallasa wadanda su ka nemi kujerar sa tun kafin ya bar Duniya – Shehu Sani

Shehu Sani ya fito ya bayyana cewa ya kamata Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadawa Duniya wadanda su ka nemi kujerar Mataimakin Shugaban kasa a lokacin da yake jinya kwanaki a Kasar waje.

Ya kamata Buhari ya fallasa wadanda su ka nemi kujerar sa tun kafin ya bar Duniya – Shehu Sani

Shehu Sani ya nemi a bayyana wadanda su kayi ta harin kujerar Osinbajo
Source: Depositphotos

Sanatan da ke wakiltar Yankin Jihar Kaduna a Majalisar Dattawa, Shehu Sani yayi wannan jawabi ne bayan da Shugaban kasar ya fito ya bayyana cewa akwai wadanda su ka ci burin samun kujerar Yemi Osinbajo a lokacin da bai da lafiya.

‘Dan Majalisar yayi wannan kira ne a shafin sa na Tuwita kwanan nan inda ya nemi Shugaban kasar yayi ta maza ya fito da sunayen ‘Yan siyasar da su ka rika zuwa fadar Shugaban kasar domin a ba su mukamin Mataimakin Shugaban kasa.

KU KARANTA: Osinbajo ya gana da wasu manyan Gwamnonin APC 3 a Villa

Fitaccen Sanatan yace muddin Buhari da Mataimakin na sa ba su fallasa wadanda su ka nemi su gaje kujerar Osinbajo ba a lokacin da Shugaba Buhari yake jinya ba, babu yadda za a yi Duniya ta san su har sai nan gaba bayan batun ya shude.

Shugaba Muhammadu Buhari dai yace wasu sun yi ta samun Mataimakin sa Yemi Osinbajo domin ya ba su mukamin Mataimakin Shugaban kasa a lokacin da ake rade-radin ya rasu lokacin da yayi fama da doguwar rashin lafiya a Kasar Ingila.

A wancan lokaci, wata Hadimar Shugaban kasa, Lauretta Onnochie ta bayyana cewa wani tsohon Gwamnan APC na Arewa wanda yanzu ya koma PDP yana cikin wadanda su kayi ta harin kujerar Yemi Osinbajo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel