Ba zan sake korafi a kan matsalolin Najeriya ba - Buhari

Ba zan sake korafi a kan matsalolin Najeriya ba - Buhari

A jiya, Lahadi 2 ga watan Disamba ne shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi alkawarin ba zai cigaba da korafi a kan matsalolin da gwamnatinsa da gada daga tsaffin gwamnatocin kasar ba.

A cewarsa, korafe-korafe kan rashawa da cin hanci da wadaka da dukiyan Najeriya da da gwamnatocin baya su kayi bai taimakawa gwamnatinsa ba, a maimakon raki, zai fuskanci matsalolin ne domin magance su.

Shugaban kasar ya yi wannan jawabin ne a yayin ganawarsa da 'yan Najeriya a kasar Poland a wani taro da mataimakiyar shugaban kasa na musamman kan harkokin kasashen waje, Abike Dabiri ta shirya a ziyarar da ya kai kasar domin hallartar taron dumaman yanayi.

Ba zan sake kokawa kan matsalolin Najeriya ba - Buhari

Ba zan sake kokawa kan matsalolin Najeriya ba - Buhari
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Shugabanin kabilar Yarabawa sun goyi bayan Atiku

Ya ce, "mun tarar da matsaloli da yawa, yanzu na ce ba zan sake yin korafi ba saboda ni na nemi mulkin da kai na. Na yi kokarin zama shugaban kasa har sau uku banyi nasarar ba sai a karo na hudu nayi nasara, saboda haka bai kamata inyi korafi ba"

"Wane ya aike ni? Sau uku ina karewa a kotun koli. A karo na ukun na ce akwai Allah, karo na hudu kuma na ce akwai Allah da kuma fasahar ta hanyar amfani da katin zabe da na'urar tantance masu zaben, hakan ya hana yin magudin zabe kuma na yi nasaea," a cewar shugaban kasar.

Buhari ya kuma bayyana farin cikinsa kan halaye na gari da 'yan Najeriya ke nunawa a kasar Polland duk da kallubalen da suke fuskanta na musamman nuna banbancin launin fata.

Kamar yadda ya saba fadin gaskiya, Shugaba Buhari ya shaidawa mahalarta taron cewa zai yi iya kokarinsa wajen amsa tambayoyinsu duk da cewa ba dole bane su gamsu da dukkan amsoshin da zai basu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel