APC: Fastocin surikin Rochas da Buhari a jam'iyyar AA sun cika jihar Imo

APC: Fastocin surikin Rochas da Buhari a jam'iyyar AA sun cika jihar Imo

Akwai kwararan alamu da ke nuna cewar Uche Nwosu, tsohon shugaban ma'aikatan jihar Imo kuma suruki ga gwamna Rochas dake neman takarar gwamna a APC ya canja sheka zuwa jam'iyyar AA.

Hakan ta fito fili a bayyane ne bayan wayar gari da ganin fastocin Nwosu tare da na shugaba sun mamaye ko ina a jihar Imo.

Faruwar hakan ta kawo karshen duk wani hasashe da canki-in-canka a kan makomar surikin na Rochas bayan jam'iyyar APC ta hana shi tikitin takarar gwamna.

APC: Fastocin surikin Rochas da Buhari a jam'iyyar AA sun cika jihar Imo

Fastocin surikin Rochas da Buhari a jam'iyyar AA sun cika jihar Imo
Source: Twitter

Majiyar mu ta shaida mana cewar an fara ganin fastocin Nwosu a garin Owerri tun yammacin jiya, Lahadi, 2 ga watan Disamba, ranar da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) za ta rufe karbar sunayen 'yan takarar gwamna daga jam'iyyu.

DUBA WANNAN: Na albarkaci abinda su ka yi - Gwamnan APC ga wadanda suka fita daga jam'iyyar

Rochas Okorocha ne ya kafa jam'iyyar AA kafin ya canja sheka zuwa PDP, sannan daga bisani ya koma APC.

A ranar 31 ga watan Janairu ne hukumar zabe za ta fitar da jerin sunayen 'yan takara a kowacce jam'iyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel