Na albarkaci abinda su ka yi - Gwamnan APC ga wadanda suka fita daga jam'iyyar

Na albarkaci abinda su ka yi - Gwamnan APC ga wadanda suka fita daga jam'iyyar

Gwamnan jihar Ogun,m Sanata Ibikunle Amosun, ya bayyana cewar dan takarar sa da APC ta hana tikitin takarar gwamna, Adekunle Akinlade, ya yi daidai da canja sheka zuwa jam'iyyar APM.

Duk da daurin gindin gwamna da yake da shi, Akinlade ya sha kasa a hannun attajirin dan kasuwar man fetur, Dapo Abiodun, a zaben fidda 'yan takara na jam'iyyar APC.

Akinlade ya ce ya canja sheka zuwa jam'iyyar APM tare da 'yan majalisar dokokin jihar Ogun 26 a yau, Litinin.

Fusatattun mambobin jam'iyyar ta APC a jihar Ogun sun bayyana, ta bakin kakakinsu, Lamidi Olatunji, cewar sun canja sheka zuwa jam'iyyar APM ne domin cika burinsu na yin takara bayan an yi ma su fashin tikitin takara a APC.

Na albarkaci abinda su ka yi - Gwamnan APC ga wadanda suka fita daga jam'iyyar

Buhari da Amosun
Source: Facebook

Ma su canja shekar da dan takarar gwamnan da su ka hada Dayo Adeneye (kwamishinan yada labarai) da Modupe Mujota (kwamishinan ilimi), sun shiga ganawa da Amosun jim kadan bayan sanar da ficewar su daga APC.

DUBA WANNAN: Tsohon gwamnan PDP ya musanta mallakar manyan kadarori da EFCC ta bankado a Kaduna

Da yake magana yayin ganawar ta su, Amosun ya bayyana cewar sau 28 yana ganawa da Buhari da shugabannin jam'iyyar APC a kan rikicin tikitin takarar gwamna a jihar Ogun.

Gwamnan ya ce Akinlade ne dan takarar da zai goyawa baya a zaben shekarar 2019 tare da bayyana cewar shine ya ba su shawarar su fita daga APC saboda rashin adalcin da jam'iyyar ta yi ma su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel