Jam’iyyar PDP ta zargi an sace naira tiriliyan 11 a gwamnatin APC ta Buhari

Jam’iyyar PDP ta zargi an sace naira tiriliyan 11 a gwamnatin APC ta Buhari

Jam’iyyar adawa ta PDP, tayi zargin wai kimanin kudi naira biliyan dubu daya, watau naira triliyan goma sha daya ne aka sace daga lalitar gwamnatin Najeriya a karkashin sa idon shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ake yi ma ikirarin mai gaskiya.

Legit.com ta ruwaito karin rigima shine PDP ta yi zargin an wawure kudaden ne daga bangaren albarkatun man fetir, inda shugaban kasa Buhari yake rike da mukamin babban ministan man fetir.

KU KARANTA: Gangamin PDP: Atiku, Saraki, Dogara da sauran jiga jigai sun dira jahar Sakkwato

Haka zalika PDP ta kalulabalanci shugaba Buhari ya bayyana ma yan Najeriya inda aka karkatar da kudaden da aka ware domin sayo ma dakarun Sojin Najeriya makamai don su yaki da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram.

Kaakakin jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar daya fitar a ranar Talata 3 ga watan Disamba, inda ya zargi Buhari da nuna halin ko in kula da yadda yan ta’adda suke kashe Sojojin Najeriya, da ma sauran sassan kasar.

“Ya kamata ace zuwa yanzu mun fara samun amsoshi daga wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari musamman game da batun kudi naira triliyan 11 da aka sacesu a gwamnatinsa, musamman a bangaren arzikin man fetir inda yake minista.

“Haka zalika muna bukatar amsa daga wajensa game da karkatar da kudin makamai da aka ware ma rundunar Sojin Najeriya da kuma albashi da alawus alawus na Sojoji, a yanzu muna zargin an karkatar da kudaden ne don gudanar da yakin neman zabensa da yake yi a zaben 2019.

“Dole ne Buhari ya bayyana dalilin rashin iya mulkinsa, wanda yayi sanadiyyar fadawar Najeriya cikin halin tabarbarewar tattalin arziki, kuma ya janyo tsadar rayuwa a Najeriya, sai Buhari ya bayyana mana yadda matasan miliyan 30 suka rasa aiki a shekarar nan.” Inji shi.

Daga karshe kaakakin ya gargadi gwamnatin shugaba Buhari da ta daina shirya karairayi da kage kage akan Atiku Abubakar da nufin bata masa suna a idanun yan Najeriya kawai don yana takarar kujerar Buhari, wannan ya nuna Buhari da kansa ya karaya da Atiku ne, a cewar Kola.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel